24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Kishi yasa matar aure ta halaka ɗiyar kishiyarta da maganin ɓera a Katsina

LabaraiKishi yasa matar aure ta halaka ɗiyar kishiyarta da maganin ɓera a Katsina

Ƴan sanda a jihar Ƙatsina sun cafke wata matar aure mai suna Aisha Abubakar, bisa zargin halaka ɗiyar kishiyar ta mai shekara huɗu, da maganin ɓera a cikin wata ƙaramar hukuma a jihar.

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Talata 17 ga watan Agusta, 2022, a garin Rimi cikin ƙaramar hukumar Rimi ta jihar.

Matar na zaman doya da manja da kishiryarta

A cewar mazauna garin, Aisha da mahaifiyar yarinyar na zaman doya da manja tun bayan da aka auro ta a matsayin kishiyar ta. Ta yanke shawarar halaka yarinyar mai suna Aisha domin ta cusa mata baƙin ciki.

A lokacin da ta shiga hannun ƴan sanda, Aisha ta bayyana cewa ta halaka yarinyar ne lokacin da mahaifiyarta tayi tafiya.

Mahaifiyarta tayi tafiya inda tabar ta a hannuna, hakan ya bani damar sanya mata maganin ɓera a cikin abinci.

Na kasance cikin baƙin ciki na fiye da shekara huɗu, domin kafin mijina ya auro ta a matsayin ta biyu, ya kora ni gida kafin daga baya ya dawo da ni.

Na halaka ta ne domin na huce haushi sannan na sanya mahaifiyarta da mijina haushin da naji nima.

A cewar matar auren

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ƴan sandan jihar, SP Gambo Isa, yace za a tura lamarin kotu da zarar an kammala bincike.

Yadda wata mata ta yankewa saurayinta mazakuta kan yunkurin yiwa ƴar ta fƴaɗe

A wani labarin na daban kuma, wata mata ta yankewa saurayinta mazakuta bisa yunƙurin yiwa ɗiyar ta fyaɗe. Matar ta sanya wuƙa mai kaifi ta yanke masa mazakuta bayan ta kama shi dumu-dumu yana ƙoƙarin keta haddin ɗiyar ta.

Wata mata mai shekara 36 a duniya, ta yanke mazakutar saurayin ta mai shekara 32 a duniya, da wuƙa bisa zargin ƙoƙarin yiwa ɗiyarta mai shekara 14 a duniya fyaɗe.

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa lamarin ya auku ne a yankin Lakhimpur Kheri, a jihar Uttar Pradesh ta ƙasar Indiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe