27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Yadda wata mata ta yankewa saurayinta mazakuta kan yunkurin yiwa ƴar ta fƴaɗe

LabaraiYadda wata mata ta yankewa saurayinta mazakuta kan yunkurin yiwa ƴar ta fƴaɗe

Wata mata mai shekara 36 a duniya, ta yanke mazakutar saurayin ta mai shekara 32 a duniya, da wuƙa bisa zargin ƙoƙarin yiwa ɗiyarta mai shekara 14 a duniya fyaɗe.

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa lamarin ya auku ne a yankin Lakhimpur Kheri, a jihar Uttar Pradesh ta ƙasar Indiya.

Tare matar da saurayin suke rayuwa

A cewar jami’ai, matar da ƴar ta suna rayuwa tare da mutumin na tsawon shekara 2 bayan ta rabu da tsohon mijinta mai shan giya.

Matar wacce ta shaidawa Times of India cewa tana aiki ne a gona lokacin da lamarin ya auku.

Tayi iƙirarin cewa ta isa gida akan lokaci inda ta kama saurayin nata dumu-dumu yana ƙokarin yin fƴaɗe ga ɗiyar ta.
Matar ta kuma ce ita ma yayi ƙoƙarin kai mata hari.

Ina ƙoƙarin ceto ƴa ta ne kawai sai hannu na ya kai kan wuƙa na yanke masa mazakuta domin na koya masa hankali. Ko kaɗan ban yi nadamar abinda na aikata ba.

Hukumomi sun yi ƙarin haske kan lamarin

A cewar jami’in SHO na ofishin yan sandan Lakhimpur, an saka saurayin cikin jerin masu aikata fyaɗe a bisa dokar POCSO.

SHO ɗin ya kuma ƙara cewa wanda ake zargin yana cikin matsanancin halin da ƙila sai an kai shi zuwa birnin Lucknow domin cigaba da duba lafiyar sa.

Har yanzu dai ba a sani ba ko za a tuhumi matar bisa laifin yankewa saurayin nata mazakuta.

Yadda ɗan aikin gida ya ɗirkawa ɗiyar mai gida ciki, ya ƙona ta ƙurmus bayan zubar da cikin

A wani labarin na daban kuma, wani ɗan aikin gida ya ɗirkawa ɗiyar mai gida ciki, sannan ya ƙona ta bayan ya zubar da cikin.

Hukumar ƴan sandan jihar Bauchi ta cafƙe wani ɗan aikin gida mai shekara 27 bisa halaka ɗiyar mai gidan sa mai shekara 13 bayan ya ɗirka mata ciki.

Wanda ake zargin, Munkaila Ado, ya ɗirka wa yarinyar ciki sannan ya haɗa baki da mahaifiyar ta domin kai ta jihar Gombe a zubar da cikin. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe