27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Momo ya sha ihu a kasuwa bayan amshe N10,000 da ‘Dan-ga-ruwa’ ya biya shi na barnar da ya masa

LabaraiKannywoodMomo ya sha ihu a kasuwa bayan amshe N10,000 da 'Dan-ga-ruwa' ya biya shi na barnar da ya masa

Jarumi Aminu Sheriff, wanda aka fi sani da Momo ya sha ihu a kasuwar singa da ke Kano bayan wani ya yi masa barna a motarsa.

Wani bidiyo wanda Tashar Tsakar Gida ta wallafa ya nuna yadda jarumin ke kirga kudi N10,000 a cikin kasuwa yayin da jama’a su ke yi masa ihu.

Kamar yadda aka gani, ya na sanye ne da babbar riga da hula yayin da wani da ake zargin mai tura kurar ruwa ne ya mika masa kudin ya amshe, ya kirga, sannan ya zuba a aljihu.

An ga yadda aka fasa masa kwalbar fitilar motarsa inda ake zargin hakan yasa ya tsaya tsayin-daka har sai an biya shi.

Bayan ya amshe kudin ya shige mota ne aka dinga yi masa ihu yayin da wasu ke kiransa da “Dan wahala”.

Lamarin ya fusata matasan wadanda da alamu su na kallon kamar ya fi karfin amsar kudin kuma ko da ma yana da bukatar, bai dace ya amsa a hannun dan-ga-ruwa ba.

Ya sha ihu kwarai kuma da alamun ko a jikinsa don ba tare da ya nuna bacin rai ko kuma ya mayar wa da kowa martani ba yayi shigewarsa mota ya tsere.

Tsadar kayan abinci: ‘Yan kasuwa su taimaka su rage farashin kayan abinci kafin Ramadan, Sarkin Musulmi

Sarkin musulmi, Muhammad Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya akan kawo mafita dangane da tashin farashin kayan abinci a kasar nan, LIB ta ruwaito.

Yayin jawabin rufe taron gasar karatun Al’Qur’ani mai girma da aka yi a Jihar Bauchi, ranar Asabar, 26 ga wata Maris din shekarar 2022, Sultan ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi gyara akan tabarbarewar tattalin arziki musamman ganin watan Ramadan ya karato.

Basaraken ya tunatar da shugabannin siyasa cewa ‘yan Najeriya sun zabe shi ne don su yi musu aiki, ya roki masu sayar da kayan abinci akan su sassauta farashin kayan abinci lokacin azumi.

Kamar yadda yace:

“Ina tunanin ya rage mana akan mu hade kawunanmu don yin aiki akan tashin farashin kayan abinci, saboda kowa ya samu ya siya a lokacin Ramadan.

“Na yarda da cewa wannan bukatar bata gagari gwamnati ba. Don mun zabe su ne don suyi mana aiki ba wai muyi musu aiki ba.

“Ina son tunatar da ‘yan kasuwa cewa su ji tsoron Allah akan yadda suke sayar da kayan abinci. Kuma sai Allah ya tambayesu a ranar Tashin alkiyama.

“Maimakon kara farashin kayan abinci da sauran abubuwa, suyi kokarin rage farashin don samun rahamar Ubangiji.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe