34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Asiri ya tonu: An cafke wani mutumi na ƙoƙarin aika bindigu zuwa Kano daga Abuja

LabaraiAsiri ya tonu: An cafke wani mutumi na ƙoƙarin aika bindigu zuwa Kano daga Abuja

Mambobin ƴan sintiri a tashar motar Zuba da ke babban birnin tarayya Abuja, sun cafke wani mutum da bindigogi takwas da ya yi niyyar kai su jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban ƴan sintirin da ke yankin, Yahaya Madaki, yana cewa lamarin ya auku a ranar Laraba da misalin ƙarfe biyu na rana, inda wanda ake zargin yazo wata tashar mota a bakin titi kusa da wani gidan mai, wanda a da aka fi sani da Dan-Kogi, yana neman motar da zata Kano.

Daga nan sai aka haɗa shi da direban da ke lodi zuwa Kano a lokacin ya miƙa masa sakon wanda aka rufe a cikin kwali da kuma lambar wayar mutumin da zai ba saƙon idan ya isa Kano.

An caji mutumin naira dubu 10 a matsayin kuɗin dakon kayan, wanda nan take ya ciro ya bayar, daga nan ne sai direban motar ya nemi sanin abinda ke a cikin kwalin inda mutumin yaƙi yarda. Ana cikin haka kawai sai mutumin ya nemi ya ranta a na kare sai akayi caraf da shi.

A cewar Yahaya

Yahaya Madaki ya ƙara da cewa ko da aka bude kwalin an ga bindigu ƙirar AK-47 guda biyar, da ƙananan bindigu uku.

DPO ɗin Zuba, CSP Osor Moses, shine ya jagoranci tawagar ƴan sandan da suka kama wanda ake zargin.

Ƙoƙarin jin ta bakin ƴan sanda yaci tura

Ko da wakilin jaridar ya nemi jin ta bakin DPO ɗin, sai yaƙi cewa komai, sai kawai ya tura shi ya tuntuɓi ofishin hukumar na Abuja.

A na ta ɓangaren, kakakin hukumar ƴan sandan Abuja, Josephine Adeh, tayi alƙawarin yin bincike kan lamarin kafin ta ce komai, sai dai har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoton, ba aji daga gare ta ba.

Hukumar KAROTA tayi babban kamu, ta cafke babbar mota maƙare da giya a jihar Kano

A wani labarin na daban kuma, hukumar KAROTA ta cafke wata babbar mota maƙare da giya a Kano.

Hukumar KAROTA ta jihar Kano, ta samu nasarar tare wata motar dakon ƙaya maƙare da giya wacce takai darajar maƙudan kuɗaɗe har N50m.

Kakakin hukumar, Nabilusi Abubakar, ya bayyana cewa giyar takai kiret 2000 a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 28 ga watan Yulin 2022.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe