
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a ranar Laraba ya tabbatar da sako DSP Usman Ali, jami’in kula da ofishin ‘yan sanda na Magami da ke Gusau daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jamilu Birnin-Magaji, sakataren yada labaran gwamnan ya fitar.
Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da DSP Ali a ranar 12 ga watan Agusta a hanyar Gusau zuwa Dansadau na jihar Zamfara.
Sai dai gwamnan ya tabbatar da sakin Dansandan ta hanyar kokarin da rundunar da ke kula da harkokin tsaro a jihar ta gabatar,tare da gabatar da jami’in da aka sace a gaban gwamna cikin koshin lafiya.
Mista Matawalle a lokacin da ya karbi bakuncin jami’in, ya bayyana jin dadinsa da matakan da gwamnati ta dauka na magance ‘yan fashi da garkuwa da mutane a jihar.
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Kwamishina a jihar Nasarawa,da Dansa
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar Nasarawa Yakubu Lawal da dansa Musab Lawal.
An sace su ne da misalin karfe tara na daren, Litinin a gidan kwamishinan dake GRA, Nasarawa Eggon.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Rahman Nansel, kamar yadda BBC Hausa da PREMIUM TIMES suka tabbatar da faruwar lamarin.
A ranar Litinin, 15 ga watan Agusta da misalin karfe 8:45 na dare hankalin ‘yan sanda da ke sintiri na yau da kullum ya kai ga karar harbe-harben da ke gudana a karamar hukumar Nasarawa-Eggon da ke jihar. Adesina Soyemi, kwamishinan ‘yan sanda (CP) ya nemi hadin gwiwar rundunar ‘yan sanda, sashin yaki da masu garkuwa da mutane, jami’an soji, ‘yan banga da kuma mafarauta na cikin gida.
“Da isar sa wurin, an gano cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, yayin da suke ta harbe-harbe, inda suka mamaye gidan kwamishin, tare da awon gaba da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba. Ana ci gaba da gudanar da aikin neman su tare da rundunar hadin gwiwa karkashin jagorancin kwamandan yankin Akwanga, ACP Halliru Aliyu, domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da damke wadanda suka aikata laifin.”
Mista Nansel ya yi kira ga jama’a da su taimaka wa ‘yan sanda da bayanan inda masu garkuwar suke.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: