34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Auren kanwata da mijina yayi ya kara mana dankon zumunci da kaunar juna, cewar Uwargida

LabaraiAuren kanwata da mijina yayi ya kara mana dankon zumunci da kaunar juna, cewar Uwargida
  • Desire Cipimo ya haifi yara 9 da matarsa ta biyu, wacce kanwa ce ga matarsa ta farko wacce ya haifi da daya da ita
  • Mutumin dan kasar Congo ya bayyana yadda ya auri matarsa ta biyu kasancewar yana son yara dayawa yayin da ta farkon ta kasa
  • Yanzu haka su na zaune lafiya kuma su na zaune cikin Zuni ci da juna kuma babu ko alamar kishi a tsakaninsu

Desire Cipimo, wani matashi ne da ya auri mata 2 wadanda uwarsu daya uba daya kuma ba tagwaye bane, Yen.com.gh ta ruwaito.

Mutumin ya fada tarkon soyayyar ‘yan uwan junan, wanda shi din shugaban kauye ne, kuma har sun haifi yara 10.

Yayin tattaunawa da Afrimax English, Desire ya bayyana yadda ya auri matarsa ta farko, Goreth, inda su ka haifi yara biyu amma daya ya kwanta dama a ranar zagayowar haihuwarsa.

Bayan shekaru 12 ba tare da ta kara haihuwa ba, mutimin ya auri matarsa ta biyu wacce kanwa ce ga matarsa ta farko, Mawazo, wacce yanzu haka yaransu 9 da ita.

Shekarun dan Desire na farko 32 yayin da autansa ke da shekaru 2 a duniya.

“Mu na ta kokarin haihuwar wasu yaran amma abin ya ci tura duk da yadda muka dinga neman magunguna iri-iri. Hakan yasa na auri kanwarta,” a cewar Desire.

Goreth ta ce bata daukar kishiyarta a matsayin kishiya face kanwa. Kuma aurensu da mijin yayi ya kara musu karfin zumunci.

Yanzu haka su na ayyukan gida tare da kuma tallafa wa mijinsu don taso da yaransu. Hakan yasa Goreth ta shawarci mata da su dena nuna wa kishiyoyinsu kishi sai soyayya.

“Idan miji yana son ki, ko da ya auri wata zai ci gaba da nuna miki kulawa da soyayya a ko da yaushe. Don haka ku dinga bai wa maza damarsu,” a cewarta.

Yadda na ritsa mijina yana lalata da mata 8 akan gadon aurenmu, Matar aure

Wata mata wacce muryarta ta dinga yawo a kafar sada zumuntar zamani ta TikTok a kwanakin baya inda ‘yan mata su ka dinga hawa muryarta ta bayyana yadda ta ritsa mijinta da mata 8 akan gadon aurensu.

Kamar yadda bidiyon wanda shafin lucky Udu ya wallafa a Facebook, an ji yadda matar take bayani dalla-dalla inda tace an samu wannan muryar tata ne a jawabin da tayi a kotu.

A cewarta, mijin nata baya aikin fari balle baki, sai shaye-shaye da bin mata, amma a wannan karon abinya ta’azzara don ta dawo daga tallar magungunar kwari ne ta ritsa shi da mata 8.

A cewarta, shigarta dakin ke da wuta ta ji sautinsa da na matan, sai ta karasa ciki taji yana canja matan yayin da ya ke lalata da dukansu kamar yana canja zannuwa.

A cewarta, mamaki ne ya kama ta hakan yasa ta nemi jin wannan ba’asin, sai ya gaura mata mari tare da ce mata kada ta dinga shiga harkokin da basu shafe ta.

Ta bayyana yadda ta tattara ya nata ya nata ta tafi gidan iyayenta tare da yaranta biyu wadanda dama ita ce take kulawa da su.

Sai daga bisani ta amsa gayyatar kotu inda alkali ta nemi jin ta bakinta bayan mijin ya kai kararta wanda ta shaida cewa mata 8 ta kama shi da su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe