Wani bidiyo wanda shafin Dokin Karfe na Facebook ya wallafa, an ga wata mata tana bayyana yadda ta shiga damuwa akan rashin aure.
Kamar yadda tace, bata san irin bakin jama’a ba, amma a taimaka mata da addu’a tare da sauran ‘yan uwanta mata su samu mijin aure.
Shafin ya bayyana sunan matar Rahama Muhammad wacce tayi gajeren bidiyon tana bayyana cewa ta rasa mijin aure.
Da farko ta fara da cewa:
“Don Allah ina so ku taya mu addu’a ga kokon barar mu, na wakilci wasu mata. Bamu san baiwar da Allah yayi wa bakinku ba. Don ku iyaye ne maza, ina rokonku da Allah, don Annabi, ku mana da addu’a Allah ya aurar damu mu huta.
“Dukanmu, daga mu har ku din, don Allah ya aurar da mu. Saboda ko wanne bawa da irin harshensa. Wani idan yayi muku addu’a, Allah jira yake yace yana neman abu, sai ya amsa masa.”
Ta ci gaba da bayyana matsanancin yanayin da take na neman miji kasancewar miji ya yi wahala. Hakan yasa bakinta ya ki shuru taga dacewar ta fito ta nemi addu’a a wurin mutane.
Ga bidiyon:
Tsokacin jama’a karkashin bidiyon
Nan da nan mutane su ka hau yin tsokaci karkashin bidiyon.
Usman Tanimu Maigoro yace:
“Allah yabaki miji nagari.”
Ahmad Ubale Abdullahi yace:
“Allah don girman al’arshinka don mu’ ujuzar alkur ‘ani don sonka da shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) ka bata miji nagari da dukkan masu bukata irintata bi Rahamatika ya Arrahamar Raheemin.”
Aisha Lawal tace:
“Na dauka ba bahausa bace amma dagani sai babba wlh yaro yadauka mai karamin jari karyewa zai yi, Allah ya zaba mafi alkairi.”
Yusuf Danumma yace:
“Ya Allah mabuwayi gagara misali kabaiwa wannan yarinyar da duk wata diyar mache kabata mijin aure nagari Ameen ya Allah .”
Sani Musa FCT Abuja yace:
“Ya rahaman yarahim ya ziljilalu walikram ya haiyu ya kayumu ya malikulmulku rabbana Dan gabas da yamma ya ubangiji Allah Dan liimar da ka saukar cikin daren lailatul kadari kamar yadda wanan baiwar Allah tafito ta baiyanawa duniya bukatar ta ya ubangiji kabata miji Nagari salihe mumuni kanity taibi mai tsoron Allah mai addini mukuma da bamufito Maka Fadi bukatar muba Allah kasni muma kacikawa burinsa Na alkairi Dan sayidina rasulillahi.”
Har da diyar gwamna a masu neman mijin aure, Malam Shu’aibu mai dalilin aure
Da farko ya bayyana wa wakilin LabarunHausa.com cewa tun lokacin yana aiki a matsayin jami’in tsaro a jami’ar Bayero da ke Kano ya fara harkar hadin aure.
A cewarsa:
“Lokacin ina yawan ganin maza su na zuwa makaranta don ajiye mata ko kuma daukarsu, hakan ya kan sanya ni tambayarsu dalilinsu na yin hakan.
“Wasu su kan ce rashin aure ne duk da su na matukar so, don haka sai na fara hada mutane auratayya.
“Da farko ko sisi ba na amsa na ke hadin aure. Daga bisani na fara amsar N1, N2, N3, N5, N10 har ya kai ga yanzu ina amsar N5000.
“Kuma ina amfani da kudin ne domin zirga-zirga don idan zan yi hadin aure sai na san gidan iyayen yarinya. Sai kuma kudin da zan sanya a waya don kiraye-kiraye.”
Yayin da wakilin LabarunHausa ya bukaci sanin ko sai talakawa kadai ne ke neman hadin aure, ya ce ba haka ba ne.
“Har da diyar gwamna a cikin wadanda ta ke neman miji, amma ba zan bayyana suna ba. Kuma akwai hotonta a cikin hotunan wadanda su ka gabatar da kawunansu su na neman miji,” a cewar Malam Shu’aibu.
Ya shawarci mutane musamman masu fama da cutar kanjamau da su dinga gabatar da kawunansu don a hada su aure saboda gudun shiga mawuyacin yanayi.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com