31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Shekara ta 90 amma ban taba saduwa da ko wacce ‘ya mace ba kuma lafiya ta garau nake

LabaraiAl'adaShekara ta 90 amma ban taba saduwa da ko wacce 'ya mace ba kuma lafiya ta garau nake

Wani dattijo mai shekaru casa’in  s duniya, mai suna Baizire Jean Marie,  ya bayyana cewa a tsawon rayuwarsa bai taba saduwa da wata mace ba. 

Ban taba fita daga kauyen mu da sunan bulaguro ba

A cewar mutumin wanda Basarake ne, tun da aka haife shi bai taɓa fita waje daga ƙauyen sa ba, kuma yana fatan ya karasa sauran kwanakin rayuwarsa a kauyen nasu. 

taba saduwa
shekara ta 90 amma ban taba saduwa da ko wacce ‘ya mace ba kuma lafiya ta garau nake

Baizire din,  ya bayyana cewa yana da matakin karatun firamare amma takaddar  satifiket din bata da wani amfani a wurinsa saboda ya kasa samun wani aiki da shi.

Ban taba saduwa da ko wacce ‘ya mace ba kuma lafiya ta lau

Ya bayyana cewa, yana son ya haifi yaro kamar sauran mutane amma ba shi da mata ko budurwa kuma bai taba kwanciya da kowace mace ba.

‘Yan uwan ​​mutumin mai shekaru 90,  sun tabbatar da cewa dattijon garau yake, a  hankalin sa da jikin sa da kuma tunanin sa, amma ba su san dalilin da ya sa har yanzu bai fara alaka da kowace mace ba.

 Sun danganta yanayinsa da matsala ta aljanu, saboda  sauran ’yan’uwansa ba haka suke ba.

Budurwa tayi wuff da mahaifin tsohon saurayin ta, ta bada dalilan ta

Wata budurwa ta auri mahaifin saurayin ta mai shekaru 89 a duniya bayan ta kama saurayin nata yana cin amanar ta.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa an saka hoton budurwar mai shekaru 23 a kafar sadarwa ta Instagram. Shafin The Savoy Show shine ya saka hotunan yarinyar a kafar ta Instagram

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe