27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Kwankwaso ya nada Jibrin, Johnson a matsayin kakakin yakin neman zaben

LabaraiKwankwaso ya nada Jibrin, Johnson a matsayin kakakin yakin neman zaben
Abdulmumin Jibrin

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya amince da nadin Hon. Abdulmumin Jibrin da Ladipo Johnson a matsayin masu magana da yawun sa a yakin neman zaben sa.

An zabe su ne saboda kwarewar su

Wata sanarwa da mataimaki Kwankwaso na musamman, Ibrahim Adamu, ya fitar, ta ce an zabi masu magana da yawun ne saboda kwarewarsu ta fannin sadarwa, sadaukar da kai ga jm’iyar NNPP,sanannu ne lungu da sako.

An Abukaci su,su yada manufar jam’iyyar

Yayin da yake yaba wa sabbin masu magana da yawun sa, Mista Kwankwaso ya bukace su da su kai sakon jam’iyyar NNPP da yakin neman zabe na RMK2023 zuwa kowane lungu da sako na kasar nan.

Tsohon Dan majlisar wakilai

Mista Jibrin ya kasance tsohon dan majalisar wakilai ne, wanda ya kware wajen gudanar da yakin neman zabe da kuma harkokin jama’a.

Kwankwaso ya fasa kwai, ya bayyana abinda NNPP ta kasa yiwa Shekarau

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilin da yasa jam’iyyar ta kasa cika wata alfarma da ƴan ɓangaren tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, suka yi.

Ya kuma ce ba wani saɓani a tsakanin shi da Shekarau, ɗan takarar sanata na Kano ta tsakiya a jam’iyyar.

Kwankwaso ya musanta akwai saɓani a tsakanin shi da Shekarau
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Kwankwaso, a wata hira da BBC Hausa, yace jita-jitar dake yawo cewa akwai saɓani a tsakanin su ba gaskiya bace, inda ya ƙara da cewa babu wani abu makamancin hakan a jam’iyyar.
Yana mayar da martani ne kan labaran dake yawo cewa tsohon gwamnan na Kano zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP, bisa kasa cika masa yarjejeniyar da akayi kafin komawar sa jam’iyyar NNPP.

Kwankwaso yace:

Babu wata yarjejeniya da ba a cika ba face ta ƴan takara. Mun yi iyakar bakin ƙoƙarin mu wurin cika wannan yarjejeniyar amma lokaci ya hana

Ya bayyana dalilin da yasa jam’iyyar ta kasa cika yarjejeniƴar da akayi
A cewar sa, da yawan mutanen da ɓangaren Shekarau suka kawo domin samun tikitin tsayawa takara sun shigo NNPP ne a lokacin da INEC ba zata amince da takarar su ba.
Sai dai, yace idan jam’iyyar taci zaɓe ta kafa gwamnati, ƴan ɓangaren Shekarau za su samu muƙamai masu gwaɓi.
Kwankwaso ya ƙara da cewa hakan ba zai haifar da wata matsala ba a NNPP, inda ya tabbatar cewa babu wata matsala a tsakanin shi da Shekarau.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe