Mutane da dama sun rasa ran su bayan fashewar wani abu a wani masallaci a birnin Kabul, babban birnin Afghanistan.
A cewar BBC, fashewar ta auku ne a masallacin a ranar Laraba lokacin sallar Yamma, inda har yanzu ba a san ko mutum nawa bane suka halaka. Jaridar The Cable ta rahoto.
Hukumomi sun tabbatar da aukuwar harin
Kakakin hukumar ƴan sanda na Kabul, Khalid Zadran, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga ƴan jarida a Afghanistan, inda ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun garzaya wurin.
Limamin masallacin yana daga cikin waɗanda suka rasu sannan da dama an garzaya da su asibiti domin duba lafiyar su.
An garzaya da waɗanda suka jikkata asibiti
Asibitin Emergency NGO, a birnin Kabul, ya rubuta a shafin Twitter cewa an kwantar da mutum 27 waɗanda harin ya ritsa da su a asibitin, ciki har da yara guda biyar.
Mun karɓi mutum 27 a asibitin mu ya zuwa yanzu bayan fashewar wani abu a yankin PD17. Asibitin ya rubuta.
Akwai yara guda biyar daga cikin su, ciki hada mai shekara bakwai a duniya.
Harin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan an halaka Rahimullah Haqqani, wani babban malami a Afghanistan, a harin ƙunar baƙin wake na bam a Kabul.
Ƙungiyar ta’addanci ta Islamic State (IS) ta ɗauki alhakin halaka malamin wanda aka kai wa hari saboda yana goyon bayan karatun mata.
Taliban ta umarci mata masu gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin da su din ga rufe fuskokinsu
A wani labarin na daban kuma, Taliban ta hana mata masu gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin su dinga kulle fuskokin su.
Hukumomin Taliban a ranar Alhamis sun ba da umarni a hukumance cewar dole ne ‘yan jarida mata a dukkan kafafen yada labarai na Afghanistan da su fara rufe fuskokinsu yayin da suka fito don gabatar da shiri a gidan talabijin.
Kafofin yada labarai na cikin gida na Afganistan sune suka ruwaito a ranar Alhamis cewa an kafa wannan doka ga duk gidajen talabijin dake fadin kasar,sun kara da cewa hakan doka ne ba shawara ba.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com