37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Kada ku zabi duk wani dan siyasa da ‘yayan sa suke kasar waje suna karatu –  Inji ASUU ga yan Nageriya 

IlimiKada ku zabi duk wani dan siyasa da 'yayan sa suke kasar waje suna karatu -  Inji ASUU ga yan Nageriya 

Farfesa Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU, ya bukaci daliban Najeriya da kada su zabi ‘yan siyasar da ‘ya’yansu ke karatu a makarantun kasashen waje. 

Oloyede din ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta, yayin da yake magana a shafin yanar gizo na Tuwita na gani gaka, wanda jaridar  Premium Times ta shirya mai taken, “ASUU, da kudaden  farfado da jami’oi  in mafita.”

kada dalibai su zabi duk ‘yan siyasar da basa kishin alumma

Da yake ba da shawarar yadda za a kawo karshen yajin aikin na kungiyar ta ASUU, ya ce kada dalibai su zabi duk ‘yan siyasar da ba za su wakilci muradunsu ba.

Osodeke din ya kara da cewa ,

“Duk wanda kuka yi imani ba zai iya biyan bukatunku ba, wanda ‘ya’yansa ke   karatu a kasashen waje, kuma auke zaune a kasashen wajen, to kada ku zabe su, ina kara maimaitawa, ba kwa bukatar ku zabe su, domin ba zaku zabi mutanen da ke son ganin bayan ku ba”. 

Yajin aikin ASUU: Lakcara ta koma tallar dankali saboda neman na tuwo

Wata lakcara a fannin sadarwa ta jami’ar Uyo, Christiana Chundung Pam ta fara tallar dankali don samun na tuwo, Legit.ng ta ruwaito.

An tattaro yadda lakcarar ta samu aikin koyarwar a shekarar da ta gabata kuma ta ce za ta ci gaba da siyar da dankalin har nan da shekara 5 in har hakan zai taimaka ilimin kasar nan ya gyaru.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe