23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Wata budurwa ‘yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin masoyin ta mai dauke da cutar kanjamau domin kada a raba su

LabaraiWata budurwa 'yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin masoyin ta mai dauke da cutar kanjamau domin kada a raba su

Wata budurwa ‘yar shekara 15 a yankin  Sualkuchi, da ke birnin Assam na kasar Indiya ta yi wa kanta allurar jinin da ke dauke da cutar kanjamau na saurayinta, a jikinta bisa dalilin zurfafawa, gami da nunasoyayyar gaskiya a gareshi  .

Yadda budurwar ta hadu da masoyin nata

Rahotanni sun bayyana cewa,  matashiyar ta hadu da saurayin nata ne ta hanyar Facebook. Daga nan sai  ƙaunar  juna ta ƙaru a tsakanin su, a sakamakon hirar da suke yi akai-akai wadda ta sanya suka kara shakuwa, ta yadda suke jin cewa daya bazai iya rayuwa ba idan babu daya. 

kanjamau
Wata budurwa ‘yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin masoyin ta mai dauke da cutar kanjamau domin kada a raba su

A cewar gidan talabijin na Kalinga, masoyan sun kasance tare tsawon shekaru uku da suka wuce kafin yarinyar ta dauki wannan matsanancin  matakin. 

A can baya budurwar tayi yunkurin guduwa da saurayin

An ruwaito cewa, yarinyar ta kuma yi kokarin guduwa da masoyinta sau da dama a baya,  amma iyayenta  suna dawo da ita gida.Amma wannan danyen aiki da budurwar ta yi a wannan karon sam babu wani daga yan uwan ta ko kewaye da ya taba tsammanin kasancewar sa.

Ta yiwa kanta allurar jini mai cutar kanjamau

 Yarinyar ta yi wa kanta allurar jinin da aka dauka daga wurin masoyinta mai cutar kanjamau, ta hanyar amfani da sirinji.Bayan yan uwanta  sun sami labarin wannan lamari mai ban mamaki, sai suka yi karar  masoyin nata a gaban shari’a . 

Yanzu haka ‘yan sanda sun tsare saurayin nata,  yayin da ita kuma take  karkashin kulawar likitoci

Bayan bullar  wannan labari, Jama’a sun yi mamakin ganin yadda matasan kasar ke yanke  irin wadannan matakai  da ba su dace ba, gami  da barazana ga rayuwa.

Daga fita yawon bariki, ta dawo da tsarabar Kanjamau da tarin TB

Wani dan Najeriya ya bayyana yadda ‘yar uwarsa wacce wasu suka dawo da ita bayan kwashe shekaru 6 ba tare da an san inda take ba ta warke daga cutukan da ke damunta, LIB ta ruwaito.

Dan Najeriyan mai suna soltune ya bayyana yadda ‘yar uwarsa ta warke daga cutar Kanjamau da tarin TB

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe