Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilin da yasa jam’iyyar ta kasa cika wata alfarma da ƴan ɓangaren tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, suka yi.
Ya kuma ce ba wani saɓani a tsakanin shi da Shekarau, ɗan takarar sanata na Kano ta tsakiya a jam’iyyar.
Kwankwaso ya musanta akwai saɓani a tsakanin shi da Shekarau
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Kwankwaso, a wata hira da BBC Hausa, yace jita-jitar dake yawo cewa akwai saɓani a tsakanin su ba gaskiya bace, inda ya ƙara da cewa babu wani abu makamancin hakan a jam’iyyar.
Yana mayar da martani ne kan labaran dake yawo cewa tsohon gwamnan na Kano zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP, bisa kasa cika masa yarjejeniyar da akayi kafin komawar sa jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso yace:
Babu wata yarjejeniya da ba a cika ba face ta ƴan takara. Mun yi iyakar bakin ƙoƙarin mu wurin cika wannan yarjejeniyar amma lokaci ya hana
Ya bayyana dalilin da yasa jam’iyyar ta kasa cika yarjejeniƴar da akayi
A cewar sa, da yawan mutanen da ɓangaren Shekarau suka kawo domin samun tikitin tsayawa takara sun shigo NNPP ne a lokacin da INEC ba zata amince da takarar su ba.
Sai dai, yace idan jam’iyyar taci zaɓe ta kafa gwamnati, ƴan ɓangaren Shekarau za su samu muƙamai masu gwaɓi.
Kwankwaso ya ƙara da cewa hakan ba zai haifar da wata matsala ba a NNPP, inda ya tabbatar cewa babu wata matsala a tsakanin shi da Shekarau.
Shugabancin Kwankwaso zai kawo waraka a Najeriya -Idahosa
A wani labarin na daban kuma, mataimakin Kwankwaso ya bayyana abinda shugabancin ɗan takarar zai kawo
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria People Party (NNPP), Bishop Isaac Idahosa, ya bayyana tikitin ubangidan sa, Dr Rabiu Kwankwaso, a matsayin “tafiyar waraka” wacce zata ciro ƙasar nan daga halin ha’ula’in da take ciki.
A cewar sa, za a samu zaman lafiya, cigaba da kwanciyar hankali ne kawai idan akwai gaskiya da adalci, waɗanda yace takarar Kwankwaso zata nuna hakan.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com