34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Kasar Indiya ta saki wasu maza 11 da aka yanke wa hukunci a kan laifin yi wa wata Musulma mai juna biyu fyade 

LabaraiKasar Indiya ta saki wasu maza 11 da aka yanke wa hukunci a kan laifin yi wa wata Musulma mai juna biyu fyade 

Bayan  yanke musu hukuncin daurin rai da rai kan laifin yi wa wata musulma fyade, an saki wasu maza 11 daga gidan yari a wannan satin, bayan an shawarar ta yiwuwar sakin  su saboda yadda suka nuna sun can dabiun su zuwa na gari. 

Yadda mazan suka haikewa matar

Wasu  maza guda goma sha daya sun yi wa  matar musulma mai juna biyu fyade, a yayin wata tarzomar yan Hindu da Musulmi, a shekarar 2002,  mahukunta sun tabbatarda faruwar sakin masu laifin, a ranar Talata,  abin da ya janyo  Allah wadai daga mijin wacce aka yi wa fyaden, da lauyoyi, da kuma ‘yan siyasa.

maza 11

An sako masu laifin ne a daidai lokacin da  ‘ yan Indiya ke bikin cika shekaru 75 da kawo karshen mulkin mallakar  Birtaniya, daga gidan yarin Panchmahals da ke yammacin jihar Gujarat a ranar Litinin bayan a da an yanke musu hukunci, a farkon shekarar 2008.

An halaka mutane da yawa a rikicin Gujarat

Sama da mutane 1,000 aka kashe a rikicin Gujarat, daya daga cikin tarzomar addini mafi muni a tarihin kasar Indiya. Wacce  har  yanzu jam’iyyar yan Hindu masu ikirarin  kishin kasa ta Bharatiya Janata Party take mulki karkashin jagorancin  firaministan Indiya na yanzu Narendra Modi.

Dalilin yiwa maza 11 afuwa

Bayan la’akari da kyawawan halayyar da suke nunawa,  da kuma  tsawon lokacin da mutane 11 ɗin suka yi a kurkuku, babban jami’in Panchmahals ya ba da shawarar a sake su.

A cewar Sujal Jayantibhai Mayatra, sun yi aiki kusan shekaru 15 a gidan yari kuma sun cancanci a yafe  musu.

Bayan sun shafe shekaru 14 a gidan yarin, wadanda aka yankewa hukuncin sun cancanci a gafarta musu”,

a cewar jami’ai

.

Suma masu laifin da aka saka sun nuna jin takaici,  saboda an kashe musu ‘yan uwa da dama a tarzomar, kamar yadda mijin wanda aka kashe matar sa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Martanin mutane lauyoyi da kuma ‘yan siyasa

“Iyalanmu sun rasu kuma muna son a zauna lafiya, amma kwatsam abin ya faru, ‘yan jarida ne suka fara sanar da mu labarin sakin su, ba daga kotu ko gwamnati ba”.

A kasar da ta yi kaurin suna wajen cin zarafin mata, ‘yan siyasa da lauyoyin ‘yan adawa sun ce sakin  masu laifin,  ya ci karo da manufofin gwamnati na martaba  mata.

Ba daidai ba ne a ɗabi’a da al’ada,  a sarayar da hukuncin da aka yanke wa waɗanda aka samu da aikata munanan laifuffuka kamar  fyaden hadaka da kisan kai, wanne irin sako muke kokarin isarwa kenan ?

n ji babban lauya Anand Yagnik

Rikicin sanya hijabi a kasar Indiya ya sanya wata kwalejin gwamnati ta kori dalibai musulmai 58

A garin Shiralakoppa da ke kudancin Karnataka, dalibai 58 ne suka gudanar da zanga-zangar adawa ga hukumar kwalejin bayan da aka dakatar da su saboda sun ki cire lullubin su.

Daliban sun fito ne daga Kwalejin Gwamnati da ke Shiralakoppa. Bugu da kari, an kuma samun karin tashe-tashen hankula a gundumomin Belagavi, Yadgir, Bellary, Chitradurgam, da Shiamogga, inda dalibai sanye da hijabi da Niqab suka yi kokarin kutsa kansu cikin ajujuwa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe