27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Ana zargin jami’an DSS da lakada wa Ali Artwork (Madagwal) bakin duka tare da azabtar da shi

LabaraiAna zargin jami’an DSS da lakada wa Ali Artwork (Madagwal) bakin duka tare da azabtar da shi

Shafin Kannywood na manhajar Facebook ta saki wata budaddiyar wasika ga shugaban hukumar ‘yan sanda masu farin kaya, DSS.

Kamar yadda wasikar ta bayyana yadda Ali Artwork yayi bidiyon wayar da kai akan ta’addanci wanda hakan yasa wasu suke bibiyar rayuwarsa da ta dan uwansa.

An bayyana yadda dan uwan Alin yake rai a hannun Allah, kuma ko da Ali ya kai wa jami’an korafi tun ranar 9 ga watan Yunin 2022, ba a dauki mataki ba ya ci gaba da zuwa yana neman daukinsu.

Yau da ya koma wurinsu ne su ka zane shi tare da azabtar da shi ta hanyar sanya shi ya kalli rana. Da wannan dalilin ne ake neman daukin shugaban hukumar, Alhaji Magaji Yusuf Bichi, da ya taimaka ya yi adalci a lamarin.

Ga wasikar kamar yadda su ka wallafa:

“ZUWA GA ADALIN SHUGABAN DSS NA KASA ALH. MAGAJI YUSUF BICHI

“YAU A GARIN KADUNA JAMI’AN DSS NA KADUNA SUN YI WA SHAHARARREN ME WASAN BARKWANCI WATO ALI ARTWORK MADAGWAL DUKA DA SASHI YA KALLI RANA SABODA YA KAWO KOKEN SA AKAN WASU MATSAFA DA KE BIBIYAR RAYUWARSA DA TA DAN UWANSA DA YA KE AIKI A WANNAN MA’AIKATA DSS.

“YA SHIGAR DA KOKEN TUN RANAR 9-6-2022 AMMA KULLUM YAZO BABU AMSA MAI DADI. YANZU HAKA DAN UWAN NASA YANA NAN RAI A HANNUN ALLAH.
BAYAN ALI ARTWORK MADAGWAL YA NEMI A MUSU ADALCI AKA KI SHI NE DA YA FUSATA YAYI MAGANA SU KA CE WAI YA YI MUSU RASHIN KUNYA.

“SHI NE SUKA MAI DUKA SU KA KORE SHI DAGA WAJEN DA SHI DA DAN UWAN NASA SANNAN SU KA CE YA TAFI SHI ZAI KULA DA DAN UWAN NASA, SU BABU RUWANSU.

“A SANINMU BABAN MU SHUGABAN DSS NA KASA MUTUMIN KIRKI NE KUMA BAYA SON ZALINCI AMMA AN SAMU WASU DAGA CIKIN GURBATATTUN MUTANEN DA KE AIKI A CIKIN WANNAN MA’AIKATA TA DSS SUNA SON SU BATA MASA SUNA DA AIKINSA BAYAN KUMA AIKI NE DA YA SHIFI KARE AL’UMMAR KASA. A SANIN TALAKAWAN KASARMU YANZU JAMI’AN DSS KAWAI SUKA RAGE A NIGERIA WANDA AKE MUSU KYAKYAWAN ZATO DA KULA DA AIKINSU YANDA YA KAMATA SANNAN AN SAN MA’AIKATAR BASA KARBAR CIN HANCI KO RASHAWA.

“KO KWANAKI MA’AIKATA SUN GAYYACI ALI ARTWORK MADAGWAL HAR GARIN ABUJA TA HANYAR DAN SHUGABAN DSS NA KASA WATO MUHAMMAD BICHI AKAN YA TAIMAKA MUSU WAJEN GANIN AIKINSU YA TAFI DAIDAI TA HANYAR SANA’AR SA TA BARKWANCI YAJE YA WAYAR DA KAN JAMA’A AKAN SHA’ANIN TSARON KASA KUMA YA YARDA ZAIYI BA TARE DA AN BASHI KO SISI BA, BAI DUBA HALIN DA KASAR TAKE CIKI BA NA RASHIN TSARO AMMA YAJE YAYI VIDEO BA TARE DA YANA TSORON MASU AIKATA WANNAN LAIFI ZASU MASA WANI ABU BA SAI DAN YA DOGARA GA ALLAH SHI NE MAI TSARE BAWANSA KUMA SHI ZAI TSARE SHI.

“DUK DUNIYA TAGA VIDEO DA YAYI A TASHAR MOTA AKAN DIREBOBI BASU KARBAR SAKO BASU DUBA BA TA HANYAR HAKA AKAN IYA SAKA MAKAMAI A CIKI A KUMA KAISHI INDA BAIDACE BA KUMA YA CUTAR DA AL’UMMA. A DON HAKA NAKE ROKON BABAN MU ALH. MAGAJI YUSUF BICHI MUNA NEMAN ADALCI DAGA GARE KA A KULA DA CASE DINSU DOMIN ABUN ZAI TAIMAKI KASA DA AL’UMMAR KASAR MU NIGERIA DON KAUDA MIYAGU DAGA CIKIN AL’UMMAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W. ALLAH YA TSARE MANA KASAR MU ALLAH YA TSARE MANA AL’UMMAR MU DARAJAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W.”

Ali Artwork – Ba a kan Ummi Rahab Zango ya fara yaudarar mata ba

Fitaccen jarumin barkwancin nan Ali Artwork ya sake magana kan rikicin Adam A Zango da Ummi Rahab, inda a wannan karon ya fito ya bayyana cewa ba akan Ummi Rahab Zango ya fara zaluntar ‘yammata ba.

Sakamakon rikici dake cigaba da wakana tsakanin Adam A Zango da Ummi Rahab, wanda wasu daga cikin mabiyan jarumin da kuma magoya bayan Ummi Rahab suka yi uwa suka yi makarbiya, sirruka na cigaba da kara bayyana tsakanin jaruman.

Rikicin wanda ya samo asali sakamakon wani abu da Adam A Zango ya bayyana cewa jarumar ta yi masa, wanda har yanzu babu wanda ke da masaniya akan lamarin, jarumar ta fito tayi barazanar tona asirin Adam A Zango, inda ta ce matukar bai yi shiru da bakinsa ba za ta bayyanawa duniya wani sirri dake tsakaninsu.

A cikin makonnan ne dai muka kawo muku rahoton yadda fitaccen jarumin barkwancin nan kuma tsohon yaron Adam A Zango, Ali Artwork, ya fito ya bukaci Zango da ya fito ya janye maganarsa ta cewa Ummi ba ta da tarbiyya, idan ba haka ba za su tona asirin jarumin.

Sai dai kuma lamarin bai tsaya a nan ba, a wani rubutu da Ali Artwork ya sakee wallafa a shafinsa na Instagram ya bayyana cewa Adam A Zango ya dade yana yaudarar matan mutane, a cewar shi ba Ummi Rahab ce jarumin ya fara yaudara ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe