34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Ɓatanci: Kotu ta zartar da hukunci kan ƙarar da mawaƙin Kano ya ɗaukaka

LabaraiƁatanci: Kotu ta zartar da hukunci kan ƙarar da mawaƙin Kano ya ɗaukaka

Wata kotun ɗaukaka ƙara a jihar Kano tayi watsi da ƙarar da aka shigar akan hukuncin babbar kotun jihar ana neman a sake shari’a kan laifin ɓatanci da mawaƙi Aminu Shariff Yahaya, yayi.

Kotun ta tabbatar cewa dokar shari’ar musulunci ta jihar Kano ta shekarar 2000 bata saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya ba. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, alƙali Abubakar Mu’azu Lamido, ya yanke cewa kundin tsarin mulkin Najeriya yaba jihohi dama ta hannun majalisun jiha su samar da dokoki.

Ya yanke cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya yarda cewa akwai yancin yin addini amma bai amince wata jiha tace ga addinin ta ba.

Yahaya ya nemi kotu da tayi watsi da hukuncin da aka yanke masa

Yahaya wanda aka yankewa hukuncin kisa a wata kotun shari’ar musulunci a Kano, a watan Agusta 2022, da farko ya roƙi babbar kotun jihar Kano da tayi watsi da hukuncin.

Babbar kotun a watan Nuwamba 2022, ta soki hukuncin inda ta bayar da umurnin a sake shari’ar a kotun shari’ar musulunci, inda tayi nuni da cewa wanda ake tuhumar bai da mai kare shi a yayin da aka gudanar da shari’ar.

A halin da ake ciki, Aminu ta hannun lauyan sa Kola Alapinni, ya ɗaukaka ƙara a kotun ɗaukaka ƙara don sanin wasu abubuwa guda biyu.

Abubuwa guda biyun sune, ko alƙalan babbar kotun sun yi daidai na bayar da umurnin sake shari’ar maimakon wanke shi bayan sun soke da warware hukuncin da kotun shari’ar musulunci tayi.

Na biyu, ko hukuncin babbar kotun yayi daidai ko bai yi ba na cewa dokar shari’ar musulunci ta jihar Kano ta shekarar 2000 tana kan turbar kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

A cikin hukuncin da alƙalain uku suka zartar, alƙali Lamido da B. M. Ugo, sun bayar da hukuncin da yafi rinjaye wanda ya tabbatar da hukuncin babbar kotu na sake shari’ar saɓanin hukuncin dake adawa da hakan na alƙali na uku.

Dokar jihar Kano ta tanadi hukuncin kisa kan masu ɓatanci

Dokar shari’ar musulunci ta jihar Kano ta shekarar 2000 ta tanadi hukuncin kisa kan ɓatanci musamman wanda akayi kan Annabi Muhammad (SAW), wanda ake tuhumar wanda ake ƙarar da shi.

Tun daga dawowar Najeriya kan turbar dimokuraɗiyya a shekarar 1999, aƙalla jihohi 12 a Arewacin Najeriya suka ɗauki yin shari’ar musulunci akan wasu laifuffuka waɗanda har su kan iya kai wa ga kotun ɗaukaka ƙara ta shari’ar musulunci.

Kotu ta yankewa basarake mai mata 12 hukuncin kisa

A wani labarin kuma wata kotu ta yankewa wani basarake mai mata 12 hukuncin kisa.

An yanke wa wani basarake wanda shine dagacin ƙauyen Efen Ibom a ƙaramar hukumar Ika ta jijar Akwa Ibom, Cif Essien Matthew Odiong, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Basaraken, wanda ake kara kan laifuka huɗu na cin amana, an yanke masa hukuncin ne bisa kisan wani mai suna Udoma Udo Ubom

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe