Wanda ya kafa One Love Family, Satguru Maharaj ji, ya roƙi waɗanda ke sukar tikitin muslim/muslim na jam’iyyar APC a takarar shugaban ƙasa da mataimakin sa da su kiyayi yin hakan, inda yake cewa addini ba shine abinda ake buƙata ba wurin yin abin a zo a gani ba a kan karagar mulki.
Maharaj ji wanda yake murnar cika shekara 29 da cewa ba za a samu yaƙi ba a Najeriya, yace mafi yawancin matsalolin dake fuskantar ƙasar nan shugabanni ne suka jawo su. Jaridar Leadership ta rahoto.
Shugabanni ke mayar da ƙasar nan baya
Yace ƴan Najeriya na da hurumin jin ɗar-ɗar bisa yawaitar laifuka, inda ya roƙe su da kada guiwar su tayi sanyi akan ƙasar duk da ƙalubalen da take fuskanta.
Maharaj ji yace yakamata ace Najeriya ta samu cigaba fiye da wanda take dashi a yanzu, amma shugabannin ta sun daƙile cigaban ta
Tabbas, wani abu bai tafiya daidai a Najeriya. Muna da dukkanin abinda ake buƙata wurin ciyar da ƙasar nan gaba, amma ci baya muke samu. A cewar shi.
Maharaj ji yayi tsokaci kan rawar da addini ke takawa
Maharaj ji yace waɗanda ke sukar tikitin musulmi/musulmi na APC kawai suna neman fitina ne kawai domin addini ba shine abinda ake nema ba wurin taɓuka abin kirki akan karagar mulki.
Yace da ace addini na taka rawar gani wurin yin abin a zo a gani akan karagar mulki, da gwamnatin shugaba Buhari ta taka babbar rawa domin shugaban cikakken musulmi ne sannan mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo cikakken kirista ne.
Musulmi/musulmi: Kada wani malami ko fasto yace muku ga wanda zaku zaɓa -Keyamo
A wani labarin na daban kuma, Festus Keyamo yaja kunnen ƴan Najeriya kan sauraron malamai akan wanda za su zaɓa.
Festus Keyamo, ƙaramin ministan ƙwadago ya roƙi ƴan Najeriya da su kiyayi malaman addini masu cewa suyi la’akari da bambancin addini wurin yin zaɓe a shekarar 2023.
Hakan na zuwa ne bayan martanin wasu mutane ciki har da shugabannin kiritoci na jam’iyyar APC, na yin watsi da matakin da jam’iyyar ta ɗauka na sanya Kashim Shettima a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu. Waɗanda dukkanin su musulmai ne.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com