29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wasu matasa hudu sun nutse a gabar tekun Legas ya yin da suke tsaka da murnar cin jarabawar WAEC

LabaraiWasu matasa hudu sun nutse a gabar tekun Legas ya yin da suke tsaka da murnar cin jarabawar WAEC
Elegushi Beach in Lagos

Wasu matasa hudu sun nutse a tekun Elegushi da ke Lekki a jihar Legas a ranar Talata, kamar yadda kakakin ‘yan sanda, Benjamin Hundeyin ya bayyana.

Mista Hundeyin, Sufeton ‘yan sanda, ya bayyana a cikin wani sakon Twitter inda yake cewa matasan sun nutse “bayan sun karbi sakamakon jarrabawarsu a makaranta.”

Na yi magana game da nutsewa a ruwa. Har yanzu, iyaye ku yi magana ta fahimta da ‘ya’yan ku don gujewa rasa rai, ”ya wallafa a shafin Twitter.

A cewar wata sanarwa da jaridar RipplesNigeria ta wallafa, lamarin ya afku ne a yankin Tekun da ba kowa.
A cikin wata sanarwa da Ayuba Elegushi ya bayyana mamatan na daga cikin dalibai 10 da suka je bakin ruwa domin murnar nasarar kammala jarabawar sakandare WASSCE.

Duk da gargadin da akayiwa matasan sun yi taurin kunne game da gargaɗin da hukuma suka musu akan wani sashe na bakin tekun.

Yadda wani matashi ya rasu a sahun gaba ana tsaka da sallar Asuba

Kowa akwai sila da kuma hanyar da zai mutu kasancewar mutuwa dole ce amma sabubbanta na da yawa.

Kamar yadda Alfijir Hausa ta bayyana, wani matashi mai suna Abdulkadir Osi amma an fi saninsa da Chairman ya rasu ana tsaka da
Yana sahun farko kamar yadda majiyar ta shaida sai aka ga rai ya yi halinsa a ranar Lahadi, 14 ga watan Augustan 2022.
Kamar yadda ya samu shaida daga mutanen da su ka san sa, jam’i ba ya taba wuce shi.

Muna fatan Ubangiji ya gafarta masa zunubbansa yasa ya huta. Ameen ya Rabbi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe