- Wani fasto a kasar Zambia ya rasa ransa bayan an birne shi a kabari na tsawon uku
- James Sakara, ya dade yana bayyana cewa zai tashi bayan ya mutu irin na ‘Jesus’
- Sai dai banyan an dawo an duba kabarin, an tarar da shi a mace kamar yadda majiyoyi su ka bayyana
Wani fasto a kasar Zambia ya mutu bayan ya yi yunkurin mutuwa kuma ya tashi kamar yadda Jesus yayi, Daily Mail ta ruwaito.
Hakan yasa yasa a daure hannayensa sannan aka birne shi a kabari na tsawon kwana uku.

An tsinci gawar James Sakara, mai shekaru 22, bayan komawa don a hako kabarin a garin Chadiza da ke Zambia, wani yanki na gabashin kasar.
Sakara, fasto ne na cocin Zion, kamar yadda rahotanni su ka bayyana, kuma kafin ya nemi a birne shi, sai da ya janyo aya daga cikin Bibul sannan ya nemi a rufe shi.
Mutane ukun da ya bukaci su daure masa hannayen, sun daure shi dakyau sannan su ka birne shi a kasa, inda ya kwashe kwana uku.
Bayan haka kabarin ne aka ga gawarsa don shirin dawowarsa da ransa bai tabbata ba.
A cikin mambobin cocin da su ka taimaka wurin rufe faston, daya ya mika kansa ga ‘yan sanda.
Har yanzu ana ci gaba da neman sauran wadanda ake zargin sun tsere.
Faston ya mutu ya bar matarsa da ciki kamar yadda rahotanni su ka nuna.
Ana gama birne mai gidan karuwai, wata karuwa ta gayyaci kwastoma don lalata kan kabarinsa
‘Yan sanda a Mutare su na neman masu rakon gawar da su ka yi tsirara kafin fara lalata akan wani kabari da ke makabartar Dangamvura da tsakar rana, Hourlyhits.com ta ruwaito.
Lamarin mai ban mamaki ya auku ne a ranar Alhamis din da ta gabata yayin birniyar wani mai gidan karuwai a Mutare cikin kasar Zimbabwe.
Mummunan al’amarin ya auku ne bayan kammala birne gawar marigayi Maroni Mazvita Karinda.
Tuni jama’a su ka ji labarin wanda aka dinga yadawa a kafafen sada daban-daban bayan ‘yan rakon gawar sun yi bidiyoyi guda biyu.
Tatenda ce ta nemi wani namiji ya zo yayi lalata da ita
Bidiyon ya fara ne bayan wata mata, fitacciyar karuwa wacce aka fi sani da Tatenda ko Mai Keisha, ta fara yin tsirara tana neman wani namiji ya zo yayi lalata da ita.
Hakan ya auku ne gaban duk masu rakon gawar wadanda ba su dade da birne Karinda ba, mai gidan karuwan Sakubva, mai shekaru 45.
Nan da nan wani ya amsa goton gayyatar kuma an fahimci cewa yana yawani zama ne a kusa da titin Sakubva.
Masu rakon gawar sun hada baki su na cewa “bvisa, bvisa, bvisa, bvisa” (ma’ana tube kayanka), inda mutumin ya hau cire kaya.
Sai dai ba a samu kwararon robar yin lalatar ba
Masu kallo sun fara yi musu liki da dalar Amurka yayin da su ka kammala tube kayansu. An dakata daga lalata bayan Tatenda ta nemi yayi amfani da kwararon roba wanda babu shi a lokacin.
Daga bisani an samo shi sannan Tatenda ta ci gaba da harkar da mutumin mutane su na kara zuga su.
Dan uwan mamacin, Fungai ya ce wannan lamarin bai yi wa ‘yan uwansu dadi ba. Sun yi kokarin dakatar da su daga yin aika-aikar amma abin ya ci tura.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com