27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Kwamishina a jihar Nasarawa,da Dansa

LabaraiWasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Kwamishina a jihar Nasarawa,da Dansa
FB IMG 1660638777782

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar Nasarawa Yakubu Lawal da dansa Musab Lawal.

An sace su ne da misalin karfe tara na daren, Litinin a gidan kwamishinan dake GRA, Nasarawa Eggon.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Rahman Nansel, kamar yadda BBC Hausa da PREMIUM TIMES suka tabbatar da faruwar lamarin.

A ranar Litinin, 15 ga watan Agusta da misalin karfe 8:45 na dare hankalin ‘yan sanda da ke sintiri na yau da kullum ya kai ga karar harbe-harben da ke gudana a karamar hukumar Nasarawa-Eggon da ke jihar. Adesina Soyemi, kwamishinan ‘yan sanda (CP) ya nemi hadin gwiwar rundunar ‘yan sanda, sashin yaki da masu garkuwa da mutane, jami’an soji, ‘yan banga da kuma mafarauta na cikin gida.
“Da isar sa wurin, an gano cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, yayin da suke ta harbe-harbe, inda suka mamaye gidan kwamishin, tare da awon gaba da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba. Ana ci gaba da gudanar da aikin neman su tare da rundunar hadin gwiwa karkashin jagorancin kwamandan yankin Akwanga, ACP Halliru Aliyu, domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da damke wadanda suka aikata laifin.”

Mista Nansel ya yi kira ga jama’a da su taimaka wa ‘yan sanda da bayanan inda masu garkuwar suke.


An kama wani mutum dan kasar Nijar yana baiwa ‘yan bindigar Katsina hayar makamai – Tsohon kakakin rundunar soji

Tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya, Gen. Sani Usman (rtd.), ya yi karin haske dangane da irin rawar da baki yan kasar Nijar ke takawa wajen tabarbarewar tsaro da ke addabar kasar Najeriya .

Yadda wani dan kasar Nijar ya ci karen sa babu babbaka ajihar Katsina

Da yake magana da tashar AIT News Usman ya bada labarin wani dan Najeriya da ya zauna a jihar Katsina domin taimakawa ‘yan fashin daji.
Da yake bada labarin, Usman ya ce,

“Akwai ‘yan kasuwa da suke amfani darashin tsaro, domin samun karamar riba daga . A lokacin da gwamnan jihar Zamfara ta bukaci ‘yan jihar da su tanadar wa kansu makamai, na yi tambaya a ina za su samu kudin, saboda yawan kudin siyan bindigar AK-47 ya kai N800,000 zuwa N1,000,000.

Talaka ba zai iya siyan bindiga ba
Talaka ba zai iya siya ba. Haka kuma duk da rashin kudin, akwai masu kudi, kuma waɗannan su ne mutanen da suke kallon rashin tsaro a matsayin kasuwanci. Inda suke samar wa da yan ta’addan makamai da alburusai. Hakan ya tuna mini da labarin wani baƙo, ɗan kasar Nijar.

Ya ci gaba da cewa,
Wannan dan Nijar ya zauna a cikin al’umma, inda wasu lokutan ya kan kawo miyagun makamai, kuma a wasu lokuta ya kan ba da hayar su ga masu laifi su aikata ta’asa”.

Mutane sun yi mamaki lokacin da jami’an tsaro suka tsara shi, kuma suka gano makamai da alburusai da ya tara. Waɗannan su ne misalan halayen mutane marasa kyau.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe