31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Kwana 3 ta kwashe tana danne ni tana min fyade da sunan zata hada ni da Maryam Yahaya, Matashi

LabaraiKannywoodKwana 3 ta kwashe tana danne ni tana min fyade da sunan zata hada ni da Maryam Yahaya, Matashi

Wani matashi wanda a baya ya dade yana bayyana soyayyarsa ga jarumar Kannywood, Maryam Yahaya ya bayyana yadda wata mata ta yi amfani da soyayyarsa ga jarumar don cimma manufarta.

Shafin Labaran Kanywood na Twitter sun wallafa bidiyonsa inda a samanshi su ka ce:

“Wani babban masoyin Jaruma Maryam Yahaya mai suna El-Shanawa dan Jihar Jigawa, ya fada cikin halin ha’ula’i sanadiyyar soyayyar da yake wa Maryam Yahaya.

“Amma ku saurari bidiyon kuji daga bakinsa, don batun ba zai fadu ba. Ance waka a bakin mai ita ta fi dadi.”

Kamar yadda ya bayyana a wani bidiyo, cike da alhini yace matar ya nuna masa cewa za ta hada shi da jarumar wanda hakan yasa ya shirya ya nufi garin Kano.

Ya bayyana yadda ta zo da mota ya dauke shi inda ta rufe shi a gida har yayi kwana uku zuwa hudu duk tana ce masa Maryam din tana wasu ayyuka.

Daga bisani ta bayyana masa cewa zata hada shi da Maryam amma ta waya don jarumar tana wasu ayyuka ne ashe duk ba gaskiya bane.

Ya ci gaba da shaida cewa, ya shiga yanayin da bai taba shiga ba rayuwarsa kuma yana fatan Ubangiji ya gafarta masa tunda ba da son ransa hakan ya auku ba.

Ga bidiyonsa yana bayani dalla-dalla:

Duk randa Allah zai dauki ran Maryam Yahaya ina rokonsa ya dauka tare da nawa, Matashi

Wani matashi wanda ya bayyana kaunar da yake yiwa jarumar Kannywood, Maryam Yahaya a fili ya ce ba zai iya rayuwa a duniya ba idan jarumar bata raye.

Da haka ne yace yana fatan Ubangiji ya dauki rayuwarsa a ranar da zai dauki rayuwar jarumar.

A wani bidiyo na TikTok da matashin yayi wanda shafin Kannywood celebrities ya wallafa, an ga matashin yana bayyana sirrin da ke ransa.

Ya fara ne da cewa:

“Hakika, gaskya ni bazan iya rayuwa babu Maryam Yahaya ba, ba wai kuma ina nufin a karkashin inuwata ba.

“Ba zan iya rayuwa ba muddin bana jin motsinta, ko da a birnin kif take. Shiyasa a ko da yaushe nake addu’a, duk ranar da Allah ya tashi daukar ran jaruma Maryam Yahaya, to ya dauka tare da nawa.

“Saboda idan babu Maryam babu ni.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe