31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Wata mata mai tsananin kyamar addinin Musulunci ta musulunta 

LabaraiWata mata mai tsananin kyamar addinin Musulunci ta musulunta 

Wata likitar yara ‘yar asalin kasar Netherlands mai suna  Paulin, ta karbi addinin musulunci. 

Paulin din an  santa da kyamar addinin Musulunci inda aka jiyo ta tana cewa:

Paulin takan nemo bayanai akan musulunci kawai domin tayi batanci gareshi

“Na dade ina jin kiyayya ga addinin Musulunci, kuma ina bibiyar  dukkan kafafen yada labarai a kan duk abin da ya shafi addinin Musulunci, kuma ina karanta abubuwa game da musuluncin, inda nake samun bayanai da zan tattauna da mutane kawai domin in yi batanci ga addinin.” 

Bayan dogon nazari cikin tsanaki, sai na ji ina son wannan addini , sai na ga akwai abubuwan da suka dace da ni a matsayina na mutum, don haka nace a raina wallahi na tsani addinin musulunci,  amma akwai abubuwan da nake so a cikin sa. “

kyamar addinin musulunci
Wata mata mai tsananin kyamar addinin Musulunci ta musulunta 

Ta tsagaita tsanin kyamar addinin Musulunci bayan zuzzurfan nazari

Bayan wasu ‘yan  watanni sai na zurfafa karance-karance a kan abin da ya shafi addinin, sai kuma naji na kasa cigaba da  cewa na tsani addinin, na kasa kame kai na ga barin son addinin, inda daga nan kawai sai na musulunta. 

Addinin musulunci ya karrama mata

A da, na yi tunanin cewa Musulunci addini ne da ke zaluntar mata kuma ba ya barin su su yi rayuwa kamar ’yan Adam, amma bayan na mika wuya,  na gane cewa duk tunanina game da Musulunci da matan Musulmi ba gaskiya ba ne.

“Na gano cewa Musulunci ya ‘yanta ni, kuma ya bani hakkin saki na aure,  idan ban samu farin ciki ba, na tarar cewa a musulunci zan iya zama duk irin macen da nake so na zama.” 

Hijabi nake sanyawa ko da yaushe kuma  bana barin sa. A halin yanzu na mayar da hankali na kan rayuwa ta gaskiya  wadda na shiga, iyalina, aikina, Ubangijina da kuma kai na.

 A ra’ayina wannan daya ne daga cikin mafi yawan abubuwan da suke jan hankalin mata zuwa addinin Musulunci, wato darajar  da ake basu a addinin  Musulunci. Musulunci ya ‘yantar da mata daga tunanin cewa suna rayuwa ne kawai don su kayatar da maza. .

Sallah tafi mini komai dadi a musulunci

Pauline din ta ci gaba da cewa, :

Yanzu bayan musulunci ina da wani kyakkyawan abu mai suna sallah. Muna yin  addu’a ne sau 5 a rana da dare,  ma’ana zan huta sau 5 a rana kenan ina mai bayyana  damuwata ga Allah SWT wanda ya halicce ni,  wannan shine abin da nafi so a addinin musulunci.

Idan baku taba yin sallah ba kafin yanzu, kuje ku fara yin sallah, zata ceceku, kamar yadda nima ta ceceni. 

Fitacciyar ‘yar gwagwarmaya daga Tamil Nadu, Sabarimala ta Musulunta

Bayan karatun Qur’ani mai tsarki da tayi,Sabarimala Jayakanthan wata ‘yar kasar Indiya mai fafutukar kare hakkin bil’adama ta yi rabo ta musulunta. Sabarimala ta kasance sananniya ce a Kudancin Indiya.

Ta sami damar aikin umarah a watan Ramadan bana

Ta sami damar ziyartar kasar Saudiyya a wannan wata na Ramadan domin yin aikin Umrah saboda samun damar shiga musulunci da tayi. A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, an hangeta tana karanta kalimatu Shahada yayin da take tsaye a cikin harabar masallacin Makkah.Yanzu haka ta chanza Sunanta zuwa Fatima Sabarimala.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe