Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, wani lauya Pelumi Olajengbesi ya bukaci Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdul Samad Rabiu, da Mike Adenuga, da su biya Naira tiriliyan 1.1 da kungiyar ASUU ta bukata domin ta janye yajin aikin da take yi, domin baiwa dumbin daliban Najeriya damar komawa makaranta.
Ya kamata matsalar dubban daliban Najeriya shafi gaggan attajirai
Ya bayyana cewa , ya kamata matsalar dubban daliban da aka sa su zauna a gida har na tsawon watanni bakwai, ta taba wadannan hamshakan masu kudi.
Ya bayyana hakan ne, a yayin da yake mayar da martani ga wani tsokaci da ake yabawa cewa , Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi wanda ya ce , gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba za ta iya ciyo bashin Naira tiriliyan 1.1 don biyan bukatar kungiyar ASUU ba.
A yayin da yake caccakar Umahi din , kan kalamansa da ya bayyana a matsayin marasa kangado, Olajengbesi din ya yi zargin cewa gwamnati na karbar rancen kudade da take barnatar dasu a ayyukan baban giwa kamar jiragen kasa a maimakon saka hannun jari ta fannin ingantaccen ilimi.

gwamnatin tarayya karkashin ta gaza biyan kungiyar ASUU
Olajengbesi ya bayyana cewa,
‘ gwamnatin tarayya karkashin, Buhari ta nuna rashin amincewar ta ne ga kawo karshen yajin aikin saboda ta gaza biyan bukatun ASUU.’
Ya koka da cewa bisa la’akari da hakan zai yi kyau a yi kira ga Dangote, Otedola, Rabiu da sauran hamshakan attajirai da su kawo agaji ga dubban matasan Najeriya da suka yi wata da watanni ba su shiga aji ba.
Yajin aikin ASUU: Lakcara ta koma tallar dankali saboda neman na tuwo
Wata lakcara a fannin sadarwa ta jami’ar Uyo, Christiana Chundung Pam ta fara tallar dankali don samun na tuwo, Legit.ng ta ruwaito.
An tattaro yadda lakcarar ta samu aikin koyarwar a shekarar da ta gabata kuma ta ce za ta ci gaba da siyar da dankalin har nan da shekara 5 in har hakan zai taimaka ilimin kasar nan ya gyaru.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: