34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Ayyiriri: Ana gab da auren dan shekara 27 da budurwarsa sa’ar kakar-kakarsa, shekarunta 74

LabaraiAyyiriri: Ana gab da auren dan shekara 27 da budurwarsa sa’ar kakar-kakarsa, shekarunta 74
  • Wani matashi ya daura damarar auren sa’ar kakar-kakarsa wacce tazarar shekarun da ke tsakaninsu 47 ne
  • Shekarun matashin 27, yayin da amaryar tasa shekarunta 74, kuma budurwa ce shakaf don bata taba aure ba
  • Soyayyarsu ta yi matukar daukar hankalin jama’a kasancewar tana zage damtse wurin nuna masa soyayya

Ku shirya ganin shagalin auren wasu masoya wadanda tazarar shekarun da ke tsakaninsu 47 ne, don masu iya magana su na cewa so makaho ne, Daily Mail ce ta ruwaito.

loveeeeee
Ayyiriri: Ana gab da auren dan shekara 27 da budurwarsa sa’ar kakar-kakarsa, shekarunta 74

Duk da dai wasu daga cikin jikokin matar sun girmi angon nata, amma hakan bai kawo cikas ga soyayyar tasu ba.

Kathi Jenkins, mai shekaru 74 ta hadu da Devaughn Aubrey, mai shekaru 27 ta wata manhajar da maza da mata ke haduwa mai suna Adult Friend Finder (AFF) a shekarar 2021.

Yayin da su ka fara da lalata da juna, bayan fahimtar juna dakyau, kasancewar duk ‘yan Texas ne, sun yanke shawarar yin aure don yanzu haka an sa ranar aurensu.

Kathi ta yi murabus, kuma yaranta hudu da jikoki 13, tare da tattaba kunne 36, da jikan-jika guda daya.

Ta dai yi soyayya da maza da dama inda ta haifi yara da su, amma bata taba aure ba.

Duk da dai amaryar ta ba angon shekaru 47, amma ‘yan uwansa sun yi na’am da soyayyarsu wacce da farko zatonsu karya yake musu har sai da ya nuna musu hotunansu tare.

A bangaren Kathi, babu wanda yayi mamaki don duk ‘yan uwanta sun san yadda take kaunar bakaken fata.

Daga yaranta har jikokinta babu wanda bai yi na’am da wannan hadin nasu ba, sai diyarta daya tal.

A cewarsa:

“A wurina ta fi ko wacce mace saboda tana gogewa don rana koya min abubuwa da dama. Bamu taba fada ba, kuma tana magana ne a tsanake ba tare da hayaniya ba. Na yarda da ita dari bisa dari.”

Ya ce tana tausarsa idan ya yi fushi sannan tana tuna masa da kakarsa sannan tana da barkwanci sosai.

Ya kara da cewa ta iya soyayya kuma ta iya girki sosai. Yana matukar ganin kyawunta. Hatta tumbinta birge shi yake yi.

Iyayen budurwa sun fatattake ta bayan ta haifa musu jaririn balarabe daga dawowa Saudiyya yin aikatau

Jama’a sun tallafawa wata budurwa wacce iyayenta suka fatattaketa bayan ta haifa musu jaririn balarabe bayan ta dawo daga Saudiyya, Legit.ng ta ruwaito.

Kamar yadda wata Judy Oricho mai tallafawa masu kananun karfi ta bayyana a shafinta na Facebook, wanda Anna Awuor mai shekaru 29 ta fuskanci cin zarafi ne daga wanda take aiki karkashinsa, daga nan ta samu ciki.

“Bayan fahimtar ta kusa haihuwa ne aka mayar da ita Kenya. Daga bisani ta haihu wanda hakan yayi sanadiyyar da aka fatattake ta da jaririn balaraben da ta haifia,” inji Oricho.

Ganin hakan ne yasa ta nufi Migori tana neman tallafin wata ‘yar uwarta, ashe itama ta tashi. Hakan yasa ta nufi sansanin Migori don neman taimako.

“Tana neman ko wanne irin taimako, abinci, suttura da kuma wurin kwana tare da jaririnta,” a cewar Oricho.

Ta yi nasarar samun taimakon don mazauna Kenya da dama dun tausaya mata wanda hakan yasa wata kungiya ta tallafa mata.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe