28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Ka bar ni in mori aure na: Uba ya koka kan yadda dansa ya ki barinsa da matarsa su kadaice

LabaraiKa bar ni in mori aure na: Uba ya koka kan yadda dansa ya ki barinsa da matarsa su kadaice
  • Wani dan Najeriya ya koka akan yadda dansa ya takura masa inda ya hana sa morar aurensa
  • A cewar mutumin, dansa yana makale wa matarsa don ba ya barinsu su kebe a matsayin ma’aurata
  • Matashin ya wallafa bidiyo inda yake tabbatar wa mutane yayin da aka dinga jajanta masa akan takurar da yaron ya yi musu

Wani mutum dan Najeriya ya wallafa bidiyon dansa mai suna Orji, wanda ya takura musu tare da hana su kebewa da mahaifiyarsa a matsayin ma’aurata, Legit.ng ta ruwaito.

Bayan wallafa kalubalen da ya ke fuskanta a TikTok, ya bayyana cewa tun bayan haihuwar yaron, ba sa morar aurensu a matsayin masoya da matarsa.

Don tabbatar wa da jama’a labarin, ya wallafa bidiyonsa tare da yaron a makale da matarsa wanda duk magiyar da su ka yi ya ki barinta.

Mahaifin mai suna Orij4dad a TikTok ya ce:

“Jama’a ban san me ke faruwa ba, ko dai duk masu aure ne ke fuskantar wannan kalubalen da zarar sun haihu? Tun bayan mun haifi yaron nan, duk sanda nake son kadaicewa da mata ta sai ya bi ta.”

Jerin fitattun kasashe 5 da mace daya ke da damar auren maza dayawa a lokaci guda

Yayin da ake kai ruwa rana a kasashe da dama idan miji zai kara aure, akwai kasashen da su ke yarje wa mace auren maza da yawa a lokaci guda, The Nation ta ruwaito.

Abu ne da kowa ya sani, maza ne ke da tarihin auren mata dayawa a lokaci guda inda wasu ma ke auren mata biyu a rana daya.

A wannan labarin da mu kawo muku jerin kasashen da mace ke da damar auren maza dayawa a lokaci guda;

  1. India

A kasar India kabilar Paharis da ke yankin Jaunsarbawar a Arewacin kasar, mata na auren maza dayawa a lokaci guda. Kuma kadan daga cikin mutanen Kinnaur da Himachal su na irin wannan auren.

Mutanen Pachi Pandavas (Wadanda ‘yan uwan juna maza biyar su ka auri mace daya mai suna Draupadi, Diyar Sarki Panchala), kuma su na ci gaba da dabbaka wannan al’ada.

Har ila yau, kabilar Toda ta Nilgiris, Najanad Vellala ta Travancore da wasu daga cikin mutanen kudancin Indiya.

A she Matar 1988, jami’ar Tibet ta yi bincike inda ta gano cewa kaso 13 na mutanen Tibetan su na gudanar da wannan al’adar.

  1. Kenya

Dokar kasar bata dakatar da mace daga auren maza dayawa ba a lokaci guda. A shekarar 2013, an samu rahoto akan yadda wasu maza biyu su ka auri mace daya wacce su ke kauna.

Amaryar wacce ta gaza zaben wanda tafi so tsakaninsu ya yanke shawarar auren dukansu. Sai dai kabilar Massai sun fi kowa dabbaka wannan al’ada.

A shekarar 2013, wasu mazan Kenya su ka auri mace daya wacce su ka kwashe shekaru su na tarayya da ita.

  1. China

Yankin Tibet su na aiwatar da irin wannan auren. Akwai kabilu kamar Monpa, Tamang, Qiang, Sherpa da Lhoba. Yanzu haka har mutanen Han da Hui sun fara.

A shekarar 2008, an gano cewa akwai kauyaku da dama da ke Xigaze da Qamdo kusan kaso 20-50% inda mata su ke auren maza biyu.

  1. Nepal

Nepal wata kasa ce da ke kudancin nahiyar Asia. A shekarar 1963 ne aka haramtawa mata auren maza fiye da daya a yankin. Sai dai mutanen yankin Humla, Dolpa da Kosi har yanzu su na aikatawa don sun yi riko da al’adarsu.

Ana samun irin wannan auren ne a kabilar Nepal ta Arewa da gabas, har da Bhote, Sherpa, Newbie da sauransu.

  1. Gabon

Maza da mata su na da damar auren duk wadanda su ke so bisa dokar jinsin kasar sai dai maza sun fi yi.

A watan Mayun shekarar 2021, wata ‘Yar kasar Gabon ta auri maza bakwai. Kuma ta bayyana cewa su na zaune lafiya da su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe