31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Addu’a kalfiyan ta samun aikin yi ga masu neman aiki

IlimiAddu'a kalfiyan ta samun aikin yi ga masu neman aiki

Jaridar Islamic Information, sun wallafa wata addu’a mai cike da tarihi da kuma biyan bukatar mai nema a duk lokacin da yake neman aiki , tare kuma da garantin zai samu aikin cikin gaggawa. , idan har ya mika tawakkalin sa gurin Allah. 

Rashin aikin yi babban  abin tsoro ne, kuma a wannan lokaci, da guraben ayyuka suka yi kadan a kasuwar neman aiki, adadin masu neman aikin yana kara rubanya ko wacce rana, wanda hakan ya sa mutane da yawa  basa samun aikin yi.

addu'a
Addu’a kalfiyan ta samun aikin yi ga masu neman aiki

Addu’a daga ingantaccen asali

A kokarin da kuke yi na samun aiki, kuna iya samun addu’o’i  da yawa domin fatan samun  aiki, amma yawancinsu ba a tabbatar da sahihancin su ba. A Wannan rubutu,  mun  fitar da addu’o’in samun aiki daga Alqur’ani da wurudi wanda zaku iya karantawa a ko wanne lokaci. 

Ga addu’ar kamar haka 

dua for job 768x768 1

Ma’anar addu’ar ;

” Sai ya shayar musu ( da dabbobin su )sannan ya koma inuwa , yace ; ya ubangijina ,lallai ni na dogara da dukkan alkairin da zaka saukar a gareni”.

Yadda addu’ar ta samo asali da wanda ta fara yiwa aiki

An ambaci wannan addu’ar a cikin Al Qur’ani mai tsarki, a suratul Kasasi sura ta 28  aya ta 24, inda Annabi  Musa A.S ya yi addu’a a lokacin da ya rasa inda zai je ya tsira daga makircin   Fir’auna. Annabi Musa A.S ya kwaso ga Jiya,  ga yunwa ga rashin kudi. Sai Annabi Musa (AS) ya daga hannayensa zuwa sama ya yi wannan addu’a.

Nan take Allah ya horewa wa Annabi  Musa (AS) abubuwan more rayuwa da zasu  ishe shi har zuwa  shekaru goma na rayuwarsa. Ya kuma ba shi matar da ya aura, duk a dan takin da yayi addu’ar. 

Addu’a ta biyu kuma itace

Akwai wata adduar kuma da zaku dinga yin wurudin ta,  don samun aiki, wato ita ce  “Ya Wahhabu”

Ma’anar Ya Wahhabu shine “Mai bayarwa.”

Sau nawa zan karanta ta?

Kamar yadda muka ambata addu’a a daya da wurudi,  daya zaka iya karantawa gwargwadon yadda kakeso koda sau daya kake karantawa a rana to shima yayi kyau,  amma dai mutum ya karanta su duka da zuciya daya. 

Muna ba da shawarar karanta wannan addu’ar sau ɗaya bayan kowace sallah.

Mabiya addinin Hindu na zagin Shahrukh Khan saboda ya yiwa mawakiyar da ta mutu addu’a irin ta Musulmai

Mabiya Addinin Hindu a kasar Indiya sun yi ta zagin shahararren jarumi Shahrukh Khan kan ya yiwa mawakiyar da ta mutu addu’a irin ta Musulmai…

Anyi jana’izar mawaƙiyar Bollywood, Lata Mangeshkar, a dandalin Shivaji, birnin Mumbai na ƙasar India a ranar 6 ga watan Fabrairun 2022. Jana’izar ta samu halartar manyan jarumai daga masana’antar ta Bollywood ciki kuwa harda babban jarumi Shahrukh Khan.

A lokacin da aka ba Shahrukh Khan damar yin addu’a, jarumin ya matsa kusa da gawar inda yayi addu’a sannan ya tofa a duk ilahirin jikinta, wanda hakan dabi’a ce a cikin addinin Musulunci.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe