‘Yan sandan kasar Saudiyya sun kama Tala Safwan, wata ‘yar kasar Masar da ke zaune a birnin Riyadh, bisa wani sako da aka watsa a kafafen sada zumunta da ke dauke da batsa.
Tasirin Tala din a soshiyal midiya
Tala Safwan ‘yar asalin kasar Masar ce, wacce take da matukar tasiri a shafukan sada zumunta na kasar Masar din, kuma mai miliyoyin mabiya. Tana wallafa bidiyo ne akan manhajar TikTok da kuma YouTube, kuma ita din ta shahara a tsakanin matasan Larabawa.

A cikin wani faifan bidiyo da Tala Safwan din ta fitar a baya-bayan nan, ta fito a cikin wani faifan bidiyo tana zantawa da wata budurwa, da kalamai na batsa, ta hanyar da ta saba wa tarbiyya da kuma daga . Inda aka ji ta tana gayyatar budurwar yarinyar, ta ziyarce ta.
Yadda yar kasar Masar din ta yi kokari hilatar budurwar
Sai budurwar yarinyar ta ce ai karfe 3 na dare, ba lokacin da ya dace da ziyara bane.
Akan hakan sai Tala Safwan ta amsa da cewa
“Ko da ya fi haka ma, domin kowa ya yi barci ba zai ji abin da zan yi miki ba. Ba kuma za su ji kukan ki ba…na daga yawan jin daɗin da za mu yi.”
Majiyoyin ‘yan sanda sun ce an daukan gurfanar da matar ‘yar kasar Masar, a gaban shariah, wadda aka mika ta ga masu gabatar da kara.
Hukumar kasar Saudiyya sun kama kayan ‘yan luwadi da madigo da aka shiga da su kasar
Hukumar kasar Saudiyya ta cafke wadansu kayan roba da ake amfani dasu wajen yin madigo, da kuma kayan sakawa da ake zargin ‘yan kungiyar luwadi da madigo ne zasu yi amfani da su.
Ma’aikatar ciniki ta kafa tawagar amsu binciken irin kayan
Ma’aikatar ciniki, ita ce ta wakilta wadansu jami’ai da zasu dinga bincike da sa ido wajen ganin an binciko irin wadannan kaya, inda kuma suka yi nasarar binciko kayan, wadanda suke sanya matasa da yawa shiga aikata ayyukan madigo da luwadi.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com