Sanata Shehu Sani ya ce gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai shi ma yana bayar da gudunmawa wajen bunkasa ayyukan ta’addanci a jihar Kaduna.
Dole Gwamna El-rufai ya dauki mataki mai tsanani akan tsaro
Ya ce idan har gwamnan jihar ba zai yi wani abu mai tsanani domin yaki da ta’addanci a jiharsa ba, to hakan yana nufin shi ma, yana bayar da gudunmuwa a kan ta’addancin , kuma da alama baya sha’awar kawar da ta’addanci a jihar Kadunan. inji Sanata Shehu Sani.
Ya kara da cewa,

“gwamnatin jiha ta na shagwaba ‘yan ta’adda da yawa, wanda yin hakan, ya yi muni matuka. Wannan na daya daga cikin dalilan da ya sa na ce gwamnan na bayar da gudunmawar ta’addanci a jihar”.
Tilas Gwamnan ya rubanya kokari
Ya ce kamata ya yi gwamnan jihar ya kara kokari, fiye da yadda yake yi a yanzu, wajen yaki da rashin tsaro. Ya kuma ce Gwamna El-rufai shima yana daya daga cikin gwamnonin da suke kai hari ga duk wani wanda ya dora wa Shugaba Buhari alhakin matsalolin rashin tsaro a Najeriya.
Don haka matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a jihar Kaduna laifin Gwamna ne kuma shi za’a zarga ba wani ba.
Atiku ya siyar hannun jarinsa na Intel, ya dora laifi a kan gwamnatin Buhari
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya siyar da kadarorinsa ciki har da hannun jarinsa na Intel.
Hadiminsa na harkar yada labarai, Paul Ibe, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya saki ta ranar Litinin, mai taken ‘Atiku ya sayar da hannun jarinsa na Intels.’
Ibe ya bayyana cewa cikin dalilan Atiku na sayar da hannun jarinsa shine gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tana shirin lalata halastattun kasuwanci, jaridar Punch ta tabbatar.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com