Wata uwa yar Najeriya ta mayar da martani ga wani sako da aka wallafa a shafin Tuwita, wanda wanda a cikin sa aka ce mace mai aiki, ba matar da za’a aura bace.
Dan asalin Arewacin Najeriya ne ya fadi wannan kalamai
Wani ma’abocin shafin tuwita mai shafin @Galadima_Samaru ,daga arewacin Najeriya, shine ya yi wannan bayani a shafin sa na Tuwita , Inda yake cewa, ” ba zai yiwu mace mai aiki ta rike gida ba.”
Ga kalaman sa:
“Babu yadda mace mai son aikin zata zama mace ta gari da kuma uwa. Sam hakan ba zai yiwu ba. Gidaje da yawa sun tarwatse, saboda mata masu ra’ayin yancin kai na yammacin turai, sun yadda cewa suna da haƙƙin suyi aiki, kuma a lokaci guda suna sarrafa gidan aure, har ma kuma su zama uwa.
Ita dai gaskiya daya ce.Kuyi duba a tsanaki ga al’ummomin yammacin duniya a yau, zaku ga dukkanin su tarkace ne, saboda matan su, sun yi watsi da nauyin da ke kansu wanda Allah ya dora musu, saboda neman daukakar duniya.”
Ita mace ce mai aiki kuma yayan ta ma dole suyi aiki
Da take mayar da martani, wacce ita ma ’yar Arewacin Nageriya ce, ta ja wa maza masu irin wannan tunanin kunne da su guji zuwa neman auren ’ya’yanta mata guda biyu.
A cewarta,
“ita tsohuwar ma’aikaciyar banki ce, wacce a yanzu haka ta mallaki makaranta, kuma tana son daya daga cikin ‘ya’yan ta; ta zama likita yayin da ta biyun kuma take fata ta zama lauya , kuma ba ta son maza masu irin wannan tunanin su zo neman auren wadannan ‘ya’ya nata.”
Hukuma ta yi ram da wanda ya kona mazaunan ‘yar aikin gidansa da dutsen guga mai zafi
Rundunar ‘yan sandan Jihar Imo sun kama wani Uzoma Egbema bayan ya yi amfani da dutsen guga mai zafi wurin kona mazaunan ‘yar aikin gidansa, Chimkamso Ekeocha, mai shekaru 12 bisa zarginta da tuka keken yaransa.
An kama mutumin ne da taimakon wani mai rajin kare hakkin bil’adama, Darlington Chidera Ibekwe bayan labarin ya yadu a kafafen sada zumunta.
Wakilin Daily Trust ya tattaro yadda yanzu haka wanda ake zargin yake Sabon ofishin ‘yan sanda da ke Owerri.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, CSP Mike Abattan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce za a mayar da mutumin bangaren binciken masu laifi na musamman don daukar matakin gaba.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com