Tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya, Gen. Sani Usman (rtd.), ya yi karin haske dangane da irin rawar da baki yan kasar Nijar ke takawa wajen tabarbarewar tsaro da ke addabar kasar Najeriya .
Yadda wani dan kasar Nijar ya ci karen sa babu babbaka ajihar Katsina
Da yake magana da tashar AIT News Usman ya bada labarin wani dan Najeriya da ya zauna a jihar Katsina domin taimakawa ‘yan fashin daji.

Da yake bada labarin, Usman ya ce,
“Akwai ‘yan kasuwa da suke amfani darashin tsaro, domin samun karamar riba daga . A lokacin da gwamnan jihar Zamfara ta bukaci ‘yan jihar da su tanadar wa kansu makamai, na yi tambaya a ina za su samu kudin, saboda yawan kudin siyan bindigar AK-47 ya kai N800,000 zuwa N1,000,000.
Talaka ba zai iya siyan bindiga ba
Talaka ba zai iya siya ba. Haka kuma duk da rashin kudin, akwai masu kudi, kuma waɗannan su ne mutanen da suke kallon rashin tsaro a matsayin kasuwanci. Inda suke samar wa da yan ta’addan makamai da alburusai. Hakan ya tuna mini da labarin wani baƙo, ɗan kasar Nijar.
Ya ci gaba da cewa,
“Wannan dan Nijar ya zauna a cikin al’umma, inda wasu lokutan ya kan kawo miyagun makamai, kuma a wasu lokuta ya kan ba da hayar su ga masu laifi su aikata ta’asa”.
Mutane sun yi mamaki lokacin da jami’an tsaro suka tsara shi, kuma suka gano makamai da alburusai da ya tara. Waɗannan su ne misalan halayen mutane marasa kyau.
Mafarauta sun kashe kwamandan Boko Haram, sun kwato makamai
Wasu mafarauta da suka shahara a Borno wajen yaƙi da ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane, a farkon makon nan sun harbe wani kwamandan Boko Haram tare da mataimakinsa a lokacin da suka yi harbin bindiga a ƙauyen Shafa Taku da ke kudancin jihar, Premium Times ta ruwaito.
Kwamandojin biyu sun shahara wajen jagorantar gungun ‘yan ƙungiyar da aka haramtawa aikata ta’addanci a ƙauyukan yankin.
Daga Shaffa Taku, mayakan Islama sun tashi kowace rana don addabar jama’a a Mandaragirau a karamar hukumar Biu, Sabon Gari a Damboa da sauran ƙauyukan ƙaramar hukumar Askira-Uba.
Mazauna yankin sun ce suna karɓar haraji da ƙarfin tsiya, suna wawure kayan abinci da satar dabbobi a waɗannan al’ummomi.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: