23 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

TURKASHI :  Na auri matar baba na bayan ya mutu amma wai mutane sun ce abin kyama muka yi kuma baza mu taba haihuwa ba 

LabaraiTURKASHI :  Na auri matar baba na bayan ya mutu amma wai mutane sun ce abin kyama muka yi kuma baza mu taba haihuwa ba 

Wani mutum mai suna Umweze dan kasar Kwango ya bayyana yadda ya auri kishiyar mahaifiyarsa bayan mahaifinsa ya rasu, ya ce suna alfahari da abin da suka yi amma al’umma sun ce abin kyama ne don haka matarsa ​​ba zata taba haihuwa ba

Matar baban nasa ta haifi ya guda daya da mahaifin sa

A cewarsa, matar baban nasa, ta haifi ‘ya  guda daya tare da baban nasa, kuma sun taso tare a matsayin wa da kanwar sa, suna rayuwa mai kyau tare da iyayen nasu biyu, har Mahaifin nasa  ya rasu, ya bar su da matar uban nasa. 

matar baba
Na auri matar baba na bayan ya mutu amma wai mutane sun ce abin kyama muka yi kuma baza mu taba haihuwa ba

Yan uwansa mata, duk suka  taso,  suka yi aure aka barshi a gida shi da matar baban sa, suna zaune a gida daya.  Bayan  wasu watanni sai suka fara jin kauna ga juna har takai ga ya tambayi matar baban nasa,  ko zai iya aurenta kuma, inda babu watawata, tace eh.

Iyayen matar sun bashi auren ta

Umweze ya ce, ya je ya nemi izinin  iyayenta kuma suka bashi dama,  ya biya amaryar sadakin ta.  Bayan wani lokaci  kadan da auren,  sai al’umma suka fara cewa a hukunta su, domin wannan abin kyama ne.

Ya ce duk da cewa ba su taba haihuwa  ba, amma matarsa ​​tana daukar ciki, sai kuma tayi barin sa,  wanda mutane a cikin al’ummarsu suka ce, ishara Allah yake nuna masa saboda ya auri mahaifiyarsa.

Yadda wani mutum ya zane danfashi da makamin da yayi yunkurin ya wa matarsa fyade

Wani mutum ya lakadawa danfashi da makami bakin duka yayin da ta yi yunkurin yiwa matarsa fyade a Ondo, inda ya kwace bindigarsa, LIB ta ruwaito.

‘Yan sanda sun yi ram da Tosin Ominiyi bayan ya sace tsadaddun abubuwa a wani gida da ke Idanre, cikin karamar hukumar Idanre a jihar, sannan ya yi yunkurin yiwa wata mata fyade.

Yayin da Tosin da wasu mutane 13 suka bayyana gaban manema labarai ranar 22 ga watan Yuni, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami ya ce wanda ake zargin ya shiga gidan ne da misalin karfe 1 na dare ta taga.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe