Dr Umar Dikko Radda, dan takarar gwamnan Jihar Katsina karkashin jam’iyyar APC, ya bayyana irin gudunmawar da zai bayar don gyara akan matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Yayin tattaunawa da BBC Hausa a shirinsu na Daga Bakin Mai Ita, ya bayyana wurare daban-daban da yayi aiki, kuma a cewarsa, mawuyacin halin da mutane ke ciki ne ya ba shi kwarin gwiwar takarar.
Ya bayyana cewa:
“Ni tsohon malamin makaranta ne, tsohon ma’aikacin banki ne, tsohon shugaban karamar hukuma ne na shekaru. Na yi aiki a majalisar tarayya. Na yi aiki a National Working committee na APC na farko da aka zaba a jam’iyya a 2014.
“Na yi shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Jihar Katsina. Na yi shugaban kanana da matsakaitan masana’antu na kasa na shekara 6. Ni ne shugaban kanana da matsakaitan masana’antu na farko da aka maimaitawa kujerarsa tunda aka kafa hukumar.”
Yayin da aka tambaye shi abin da ya ba shi kwarin gwiwar neman kujerar gwamnan Jihar Katsina, ya kada baki inda yace:
“Alhamdulillah abin da ya ba ni kwarin gwiwar takara shi ne tausayawa al’umma. Saboda na yi shugaban karamar hukuma na shekara shida. Na ga halin da mutane su ke ciki.
“An shiga cikin gwamnatin nan na ga halin da mutane su ke ciki, shiyasa nake ganin akwai gudunmawar da zan iya bayarwa wajen fitar da mutane daga mawuyacin halin da su ke ciki.”
Dangane da tsaro, ya ce za su tabbatar sun ba jami’an tsaro gudunmawar da goyon bayan da su ke bukata sannan za su horar da matasa daga yankunan da matsalar t ke barkowa.
Ya bayyana cewa har da shi za a dinga farautar ‘yan ta’adda ana kama su.
Ya ci gaba da cewa:
“Sai mun yi amfani da yaran mu. Za kaga yara su na neman aikin soji. Za mu dauke su aiki, zamu horar da su, za mu siya motoci masu sulke, za mu sayi makamai. Za mu ba ma’aikata irin gudunmawar da ya kamata a ba su. Sannan kuma in an yi buruntu zan fito ayi buruntun da ni.”
An kashe shugaban ‘yan ta’adda da matansa a harin da jirgin sama ya kai jihar Katsina
Rundunar sojin saman Najeriya, ta kai wani samame da safiyar Lahadi, inda ta yi nasarar kashe shugaban kungiyar ‘yan ta’adda da ke aiki a Zamfara, Abdulkarimu Faca-Faca tare da matansa biyu da manyan kwamandojin sa takwas.
An kai farmakin ta sama ne da misalin karfe 3 na safiyar Lahadi a kauyen su mai suna Marina, a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
PREMIUM TIMES ta tattaro bayanai daga wata majiya da ke sansanin ‘Forward Operation Base (FOB)’ da ke Katsina cewa an kai harin ne bayan da jami’ansu suka samu rahoton sirri kan inda Mista Faca-Faca yake.
Kakakin hukumar ta FOB, Abdul Olaitan, bai amsa tambayoyin da aka aike masa ba game da harin, amma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isa ya tabbatar da cewa an kai harin bam a gidan shugaban kungiyar.
“An kashe ‘yan ta’adda takwas da ake zargin ‘yan ta’adda ne da suka hada da shugabansu Abdulkarim Faca-Faca a farmakin da NAF ta kai a jiya, kuma da safiyar yau a wannan yanki domin gudanar da aikin kawar da ‘yan ta’adda ,‘yan ta’addan sun gudu amma duk shanunsu sun halaka yayin da da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga. Rahotanni ya tabbatar da hakan, ”in ji Mista Isa a cikin sakon WhatsApp.
Dan majalisar mai wakiltar Safana a majalisar dokokin jihar Katsina, AbdulJalal Runka, shi ma ya tabbatar da harin.
Yan bindiga sun kashe ‘yan banga biyu, sun yi awon gaba da wasu amarya da ango a garin Katsina
Wasu ‘yan bindiga sun kashe’yan banga guda biyu tare da yin garkuwa da wasu mazauna unguwar Shola Quarters a cikin birnin Katsina da safiyar Lahadi.
Wadanda aka yi garkuwa da su a harin da ya dauki same day sa’o’i sun hada da wasu ango da amarya.
Shola Quarters anguwace da ke bayan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (Tsohon Federal Medical Center) Katsina.
Yankin wanda ya kasance a tsakiyar birnin na katsina wanda ke dauke da shaguna,gidaje har ma da ofisoshin gwamnati.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com