28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Jerin fitattun kasashe 5 da mace daya ke da damar auren maza dayawa a lokaci guda

LabaraiJerin fitattun kasashe 5 da mace daya ke da damar auren maza dayawa a lokaci guda

Yayin da ake kai ruwa rana a kasashe da dama idan miji zai kara aure, akwai kasashen da su ke yarje wa mace auren maza da yawa a lokaci guda, The Nation ta ruwaito.

Abu ne da kowa ya sani, maza ne ke da tarihin auren mata dayawa a lokaci guda inda wasu ma ke auren mata biyu a rana daya.

A wannan labarin da mu kawo muku jerin kasashen da mace ke da damar auren maza dayawa a lokaci guda;

  1. India

A kasar India kabilar Paharis da ke yankin Jaunsarbawar a Arewacin kasar, mata na auren maza dayawa a lokaci guda. Kuma kadan daga cikin mutanen Kinnaur da Himachal su na irin wannan auren.

Mutanen Pachi Pandavas (Wadanda ‘yan uwan juna maza biyar su ka auri mace daya mai suna Draupadi, Diyar Sarki Panchala), kuma su na ci gaba da dabbaka wannan al’ada.

Har ila yau, kabilar Toda ta Nilgiris, Najanad Vellala ta Travancore da wasu daga cikin mutanen kudancin Indiya.

A she Matar 1988, jami’ar Tibet ta yi bincike inda ta gano cewa kaso 13 na mutanen Tibetan su na gudanar da wannan al’adar.

  1. Kenya

Dokar kasar bata dakatar da mace daga auren maza dayawa ba a lokaci guda. A shekarar 2013, an samu rahoto akan yadda wasu maza biyu su ka auri mace daya wacce su ke kauna.

Amaryar wacce ta gaza zaben wanda tafi so tsakaninsu ya yanke shawarar auren dukansu. Sai dai kabilar Massai sun fi kowa dabbaka wannan al’ada.

A shekarar 2013, wasu mazan Kenya su ka auri mace daya wacce su ka kwashe shekaru su na tarayya da ita.

  1. China

Yankin Tibet su na aiwatar da irin wannan auren. Akwai kabilu kamar Monpa, Tamang, Qiang, Sherpa da Lhoba. Yanzu haka har mutanen Han da Hui sun fara.

A shekarar 2008, an gano cewa akwai kauyaku da dama da ke Xigaze da Qamdo kusan kaso 20-50% inda mata su ke auren maza biyu.

  1. Nepal

Nepal wata kasa ce da ke kudancin nahiyar Asia. A shekarar 1963 ne aka haramtawa mata auren maza fiye da daya a yankin. Sai dai mutanen yankin Humla, Dolpa da Kosi har yanzu su na aikatawa don sun yi riko da al’adarsu.

Ana samun irin wannan auren ne a kabilar Nepal ta Arewa da gabas, har da Bhote, Sherpa, Newbie da sauransu.

  1. Gabon

Maza da mata su na da damar auren duk wadanda su ke so bisa dokar jinsin kasar sai dai maza sun fi yi.

A watan Mayun shekarar 2021, wata ‘Yar kasar Gabon ta auri maza bakwai. Kuma ta bayyana cewa su na zaune lafiya da su.

Da ana biyan matan aure kuɗin aikin da suke yi da sun zama hamshaƙan attajirai -Jarumar fim

Jarumar a masana’antar fina-finai ta Nollywood, Mary Remmy Njoku, ta nuna adawar ta kan masu cewa wurin mata yana a ɗakin girki ne.

Jarumar ta kuma soki mutanen dake da irin wannan tunanin na cewa mata a ɗakin girki aka san su, a wani rubutu da tayi a shafin sada zumunta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Jarumar ta nuna cewa maza sun fi mata sabawa da ɗakin girki amma wanda ake samun kuɗi a ciki

Njoku wacce tayi nuni da cewa sama da kaso 78 na manyan masu dafa abinci na duniya maza ne, ta ƙara da cewa yakamata a fara jinjinawa matan aure domin da ace ana biyan su kuɗin aikace-aikacen da suke yi, da sun fi wasu shugabannin banki samun kuɗaɗe.

Ta kuma ƙara nuni da cewa maganar gaskiya itace maza sun fi mata sabawa da ɗakin girki amma ɗakin girkin da ake biya inda suka kyale mata da ɗakin girkin da ba a biya su kula da shi.

Jarumar ta rubuta a shafin Instagram ɗin ta cewa:

Yakamata mu koyi jinjinawa matan aure nagari. Domin da ace ana biyan su bisa dukkanin aiyukan da suke yi, da sun samu kuɗaɗe fiye da wasu shugabannin banki.

Jarumar na auren shahararren ɗan kasuwa

Mary Njoku na auren shahararren ɗan kasuwa kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa gidan talabijin na iROKO TV, Jason Njoku, sananna ce akan matsayar ta ganin mata sun samu gaskiya, daidaito da mutuntawa.

Za a fara biyan matan aure albashi a kasar Kenya

A wani labarin na daban kuma, matan aure za su fara samun albashi a ƙasar Kenya. Wata kotu ce dai a ƙasar ta zartar da hukuncin saboda la’akari da aikin da matan aure suke yi, ya cancanci su samu albashi.

Wata babbar kotu a kasar Kenya ta yi karin haske akan tsarin fara biyan matan aure albashi, inda ta bayyana zama matar aure a matsayin aikin yi da ya kamata a biya su albashi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe