31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Hotuna: Yadda kwararriyar mai kwalliya ya tayar da komadar tsohuwa, ta maida ta danya shakaf

LabaraiHotuna: Yadda kwararriyar mai kwalliya ya tayar da komadar tsohuwa, ta maida ta danya shakaf

Wasu hotuna da su ka bazu a kafafen sada zumuntar zamani sun dauki hankula bayan an ga tsohuwar da ta kai akalla shekaru 70 da doriya dauke da kwalliya mai daukar hankali, a shafin Makeup Artists da ke Facebook.

Da farko za ka yi tunanin yarinya ce mai kananun shekaru amma mai kwalliyar ta wallafa hotunanta kafin ta yi mata kwalliyar da kuma bayan ta yi mata.

Nan da nan mutane su ka yi caa su na mamakin kwarewar mai kwalliyar akan yadda ta mayar da tsohuwa yarinya danya shakaf.

Labarun Hausa ta bi tsokacin jama’a karkashin hotunan inda ta tsinto wasu daga ciki:

Sophia Anurika ta ce:

“Saboda me za ki zake wurin yi wa tsohuwa kwalliya? Idan fa mara yawa take so?”

Ola Maryam ta ce:

“Kin yi kokari amma ki bai wa tsohuwar shawarar ta daina shafe-shafe.”

Dimmy Jay ta ce:

“Kai! A wannan tsufar ta ki hakura da rayuwa? Ya ki daina shafe-shafe?”

Garin neman gira: Bayan kashe N1.6m likitoci sun komadar wa sarauniyar kyau fuska

Likitoci sun komadar da fuskar wata sarauniyar kyau ta kasar Rasha mai suna Yulia Tarasevich, Legit.ng ta ruwaito.

A halin yanzu Yulia Tarasevich, matashiya mai shekaru 43 bata iya rufe idanuwan ta ko murmushi bayan kashe Euro 3,000 ( miliyan N1.6) don inganta kyawunta.

Hakan yasa matar mai yara biyun ta maka likitocin da suka yi mata aikin kotu, inda tayi korafi game da yadda tazo gare su da kyakyawar lafiyayyar fuska amma suka lalata.

Da alamu matar mai shekaru 43, Yulia Tarasevich ba zata sake murmushi ko rufe idanuwan ta ba, har ta kare rayuwarta.

An bar sarauniyar kyawun ta kasar Rasha da mokadaddar fuska bayan jerin aikin da aka mata don gyara tsufanta wanda ya ja mata kashe Euro 3,000 (miliyan N1.6), amma hakan bai sa sun yi nasara ba don haka ta maka likitocin da suka mata aikin kotun.

Daily Mail ta ruwaito yadda aka wa Yulia aiki a fuska, karin mazaunai da wasu ayyuka don tsatso kyau a kwayar idanuwan ta a wani asibiti a Krasnodar dake kudancin Rasha.

Sai dai, matar mai yara biyu ta lura tun bayan aikin da aka yi mata, bata iya rufe idanuwan ta ko kuma motsi da ilahirin fuskarta balle kuma murmushi.

Hakan yasa ta kara kashe karin Euro 20,000 (miliyan N11.3) don gyara mata fuskar ta zuwa daidai.

Matar mai shekaru 43 ta taba wakiltar kasar Rasha a gasar sarauniyar kyau ta duniya a shekarar 2020. Bayan kashe Euro 20,000 ( miliyan N11.3) amma hakan baisa ta yi nasara ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe