27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Yadda ɗan aikin gida ya ɗirkawa ɗiyar mai gida ciki, ya ƙona ta ƙurmus bayan zubar da cikin

LabaraiYadda ɗan aikin gida ya ɗirkawa ɗiyar mai gida ciki, ya ƙona ta ƙurmus bayan zubar da cikin

Hukumar ƴan sandan jihar Bauchi ta cafƙe wani ɗan aikin gida mai shekara 27 bisa halaka ɗiyar mai gidan sa mai shekara 13 bayan ya ɗirka mata ciki.

Wanda ake zargin, Munkaila Ado, ya ɗirka wa yarinyar ciki sannan ya haɗa baki da mahaifiyar ta domin kai ta jihar Gombe a zubar da cikin. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Kakakin hukumar, SP Ahmed Wakil, a ranar Asabar 13 ga watan Agusta, 2022, yace an cafke wasu mutum biyu ciki har da matar da ta bayar da abin zubar da cikin. 

A cewar Wakil, bayan samun nasarar zubar da cikin mai wata huɗu, wanda ake zargin da abokin sa sun maƙare yarinyar, sannan suka ƙona jikinta ƙurmus tare da birne ta a cikin wani ƙaramin rami a cikin daji.

Mahaifin yarinyar ya shigar da ƙorafin ɓacewar ta

Kakakin ƴan sandan yace, mahaifin yarinyar wanda ya lura da cewa yarinyar sa ta ɓace kuma yana zargin ɗan aikin gidan da abokin sa, sai ya miƙa rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda na Alkaleri.

A ranar 10/08/2022 da misalin ƙarfe 9 na safe, wani Alhaji Danladi Mohammed, daga ƙauyen Mai’ari Arewa Pali, ya shigar da ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Alkaleri, cewa a ranar 04/08/2022 ɗiyar sa mai suna Safiya Alhaji Danladi ƴar shekara 13, ta bar gida inda akayi zargin ta ɓace sannan yana zargin cewa ɗan aikin gidan sa mai suna Munkaila Ado mai shekara 27 da wani Muazu Umaru mai shekara 35, sune waɗanda yake zargin sanin inda ƴar sa ta ɓace. A cewar sanarwar

Nan da nan aka fara gudanar da bincike, DPO na Alkaleri yaje wurin da aka birne yarinyar sannan aka tono ta inda aka kai ta babban asibitin Alkaleri, inda likita ya tabbatar da ta rasu

A yayin da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana cewa yarinyar budurwar sa ce kuma tana ɗauke da cikin wata huɗu da sanin mahaifiyar ta amma mahaifin ta Alhaji Danladi Mohammed bai sanda cikin ba.

Ɗan aikin gidan ya haɗa baki da mahaifiyar yarinyar

Ya kuma ƙara bayyana cewa ya haɗa baki da mahaifiyar yarinyar da abokin sa Muazu Umar, inda suka ɗauke ta zuwa Gombe domin a zubar da cikin. Daga nan ne bayan sun isa Gombe aka kai yarinyar gidan wata Hajiya Amina Abubakar mai shekara 50 a unguwar Jekada Fari a bayan asibitin ƙwararru na Gombe, inda aka ba yarinyar wasu abubuwa domin cikin ya zube.

Daga ƙarshe akan hanyar su ta ƙauyen Mai’ari kusa da ƙaramar hukumar Akko ta jihar Gombe, mutum biyun da ake zargin suka maƙare yarinyar, inda ta suma daga nan tace ga garin ku nan. Daga nan suka ƙona ta ƙurmus sannan suka birne ta a wani ƙaramin rami cikin daji a ƙaramar hukumar Akko.

A halin da ake ciki an cafke mutum biyun da ake zargin bisa cin mutunci da keta haɗɗin ɗiya mace.

Talauci ko ƙeta: Yadda aka cafke wata mata na ƙoƙarin siyar da ɗan cikinta kan kuɗi N243k

A wani labarin na daban kuma, wata mata ta shiga hannun hukuma bisa ƙoƙarin siyar da ɗan cikin ta.

An cafke wata mata bisa ƙoƙarin sayar da yaron ta mai shekara bakwai a duniya ga mutanen da bata san su ba kan kuɗi £4,000, (N243k)

Matar wacce ta haifi yara uku anyi zargin ta tallata ɗan na ta a matsayin na sayarwa a ƙoƙarin ta na biyan basussukan da ta ci.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe