31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Dalilin da yasa matata ta amince ta bani ƙodar ta -Eedris Abdulkareem

LabaraiDalilin da yasa matata ta amince ta bani ƙodar ta -Eedris Abdulkareem

Shahararren mawaƙin gambara na Najeriya, Eedris Abdulkareem, a ranar Asabar ya bayyana cewa matar sa Yetunde, itace za ta bashi ƙoda.

Mawaƙin wanda ya bayyana al’umma batun ciwon ƙodar sa a watan Yuli, ya bayyana hakan ne a wurin Freedom Vibes 6.0, wani taro domin karrama shi a Freedom Park, jihar Legas. Jaridar Premium Times ta rahoto.

Eedris Abdulkareem ya bayyana dalilin da yasa matar shi ta amince

Eedris Abdulkareem mai shekaru 48, yace:

Ina faɗa cikin tsawa ga matata, ina maganar akan lokacin farko da muka je ganin likita, likita yace basu son ana girbar ƙoda, sayar da ita da sauran su. Cewa mai bayarwan ya zama ɗan’uwa ne, ko aboki, ko ƴar ka ko ɗan ka ko kuma ƙani ko yaya

Anan take a wurin, matata ta yanke shawarar yin gwaje-gwajen da ake yi. Daga gwaje-gwajen da akai mata sun bada sakamako mai kyau cewa ƙodar da tawa za su iya haɗuwa. Saboda haka dukkan yabo ya tabbata ga Allah, sannan nagode masa da ba sai na jira shekara ɗaya ko biyu ba don nasan abu ne mai wahala.

Wannan shine karon farko da mawaƙin ya bayyana ainihin haƙiƙanin wanda zai bashi ƙoda.

Eedris ya auri matar shi a shekarar 2002. Suna da ƴaƴa uku a tare.

Kafin zuwan wannan lokacin, matar sa bata ciki bayyana kan ta ba duk da cewa tana auren sanannen mutum.

Ya nuna matuƙar godiyar sa ga waɗanda suka tallafa masa

Mawaƙin wanda ya halarci taron ta kafar Zoom, yayi jawabi mai kyau sosai.

Mawaƙin ya nuna godiyar sa inda yake cewa:

Ina son nuna matuƙar godiya ta ga matata,  Baba Dede Mabiaku, ƴar’uwa Mariam bisa assasa neman min tallafi a GoFundme, ɗan’uwa na Chidi, ɗan’uwa na E-money, Cif Allen Onyema, da dukkanin wanda ya taimaka min, ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje, da ƴan Najeriya na cikin Najeriya.

Mawaki Idris Abdulkareem ya bayyana matsanancin halin da yake ciki daga kan gadon jinyar sa na asibiti 

A wani labarin na daban kuma, Eedris Abdulkareem ya bayyana halin da yake ciki daga kan gadon jinyar a asibiti.

Shahararren mawakin nan na Najeriya Idris Abdulkareem, ya yada sabon bidiyo daga gadon sa na asibiti, inda ya bayyana matsanancin ciwon da ya addabeshi, a ranar Laraba, shida 6 ga watan Yuli. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe