31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yadda wani matashi ya rasu a sahun gaba ana tsaka da sallar Asuba

LabaraiYadda wani matashi ya rasu a sahun gaba ana tsaka da sallar Asuba

Kowa akwai sila da kuma hanyar da zai mutu kasancewar mutuwa dole ce amma sabubbanta na da yawa.

Kamar yadda Alfijir Hausa ta bayyana, wani matashi mai suna Abdulkadir Osi amma an fi saninsa da Chairman ya rasu ana tsaka da sallar asuba.

Yana sahun farko kamar yadda majiyar ta shaida sai aka ga rai ya yi halinsa a ranar Lahadi, 14 ga watan Augustan 2022.

Kamar yadda ya samu shaida daga mutanen da su ka san sa, jam’i ba ya taba wuce shi.

Muna fatan Ubangiji ya gafarta masa zunubbansa yasa ya huta. Ameen ya Rabbi.

Wani Alhaji daga jihar Kano ya rasu a Saudiyya

Wani Alhaji ɗan jihar Kano, Sani Idris Muhammad ya rasu a Saudiyya a lokacin hajjin bana na wannan shekarar 2022.

Hukumar kula da jindaɗin Alhazai ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar Alhajin a ƙasa mai tsarki. Jaridar The Punch ta rahoto.

Babban magatakardan hukumar, Alhaji Muhammad Abba-Danbatta, ya bayyana hakan ga ƴan jarida a ranar Asabar.

An bayyana garin da Alhajin ya fito

Yace Alhaji Idris-Muhammed wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Madobi ta jihar, ya rasu ne a ranar Asabar bayan wata ƴar gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti a birnin Makka.

An birne marigayin kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a maƙarbartar Shira ta masallacin Harami a birnin Makka.

Abba-Danbatta yayi adduar Allah ya jiƙan marigayin sannan ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan marigayin.

Adadin Alhazan Najeriya da suka rasu a bana a Saudiyya

Alhaji Idris Muhammad shine mahajjaci na huɗu da ƴa rigamu gidan gaskiya daga Najeriya, a yayin gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 2022.

Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi jihar Nasarawa, ta rasu a ranar 29 ga watan Yuni, bayan gajeruwar rashin lafiya inda aka binne ta a Makka, yayin da Hajiya Hasiya Aminu daga Zaria, jihar Kaduna ta rasu a ranar Arfah jim kaɗan bayan ta dawo filin Arfah.

Muma anan Labarunhausa.com muna addua’r Allah ya jiƙan su da rahama ya kuma gafarta musu ya kyautata namu ƙarshen.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe