29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Matan Gwamnonin Arewa sun yi zama akan matsalar ilimi, kalubalen shan muggan kwayoyi

LabaraiMatan Gwamnonin Arewa sun yi zama akan matsalar ilimi, kalubalen shan muggan kwayoyi
Northern governors wives meet in Kebbi

Kungiyar matan gwamnonin Arewa, NGWF, ta sanya ranar Disamba 2022 don aiwatar da wasu ayyuka da suka hada da karfafawa mata, magance shaye-shayen kwayoyi da rashin ilimi.
Shugabar kungiyar ta NGWF, Hadiza El-Rufai ce ta bayyana hakan a lokacin da take gabatar da sanarwar jim kadan bayan kammala taron kungiyar da aka gudanar ranar Asabar a Birnin Kebbi.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, matan gwamnonin Arewa 19 sun hallara a Birnin Kebbi domin wani taron kwanaki biyu don bayar da shawarwari kan shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Ta ce: “Muna so kafin wa’adin kowannenmu ya kare ya kamata ya yi wani aiki na musamman da zai magance matsalolin da ke faruwa a jihohinmu.
“An kuma amince cewa kalubalen da muke fuskanta sun hada da rashin ilimi da karfafa mata musamman a arewa kuma mun amince da samar da tsarin aiki don magance wadannan kalubale.
“Taron ya kuma amince da cewa horarwa da karfafawa masu shan muggan kwayoyi ya zama aikin da za a gudanar na kammala dukkan ayyukan mu kuma za a kaddamar da shi nan da Disamba 202
2.”
Shugabar ta kara da cewa mambobin sun amince da gayyatar ‘Nigeria For Women (NFW) Project’ domin yiwa mambobinsu bayanin ayyukansu.
Taron ya bukaci duk jihohin da ba a cikin shirin ‘At-Risk Children’ su sanya hannu domin amfanin yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma al’umma,” in ji Misis El-Rufai.

Northern governors wives at airport.jpeg

Yajin aiki: Kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta bayyana cewa jarabawar da ake yi a jami’ar Kaduna ta sabawa doka,ta nemi a soketa

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta bayyana jarabawar da ake yi a jami’ar jihar Kaduna (KASU) a matsayin saba ka’ida da ka’idojin gudanar da jarabawar a makarantun ilimi.
Kungiyar ta bayyana hakan ne ta wata sanarwa da ta fito daga shiyyar Kano, inda ta dage cewa duk wani jarrabawar da aka gudanar a halin yanzu dole ne a sake gudanar da shi domin tabbatar da karko.
A ranar 2 ga watan Agusta ne jami’ar ta koma harkokin ilimi tun ranar 14 ga watan Fabrairu lokacin da ma’aikatanta suka bi ayarin yajin aiki na bai daya da shugabannin kungiyar ASUU na kasa suka ayyana kan wasu bukatu da aka gabatar a gaban gwamnati.
Gwamnatin Jihar Kaduna ce ta kafa Jami’ar Jihar Kaduna a shekarar 2004 tare da kaddamar da dokar Jihar Kaduna mai lamba 3.
Sai dai ‘ya’yan kungiyar ASUU na jami’ar sun shiga yajin aikin ne a fadin kasar domin nuna adawa da yadda ilimin jami’o’in ke kara
tabarbarewa a Najeriya, musamman kalubalen rashin kudi da gwamnati ke fuskanta, da rashin jin dadin ma’aikata da dai sauransu.
Akwai sauran jami’o’in gwamnati a Najeriya da ‘yan kungiyar ASUU suka ki shiga yajin aikin da ake yi a fadin kasar. Sun hada da Jami’ar Jihar Kwara, Jami’ar Jihar Osun, Jami’ar Jihar Legas, da Jami’ar Ambrose Alli ta Jihar Edo, da dai sauransu.
Gwamna El-Rufai ya yi barazanar ne bayan sama da watanni biyar da ma’aikatan cibiyar suka shiga yajin aiki wanda ya bayyana hakasa matsayin hadin kai, inda ya yi kira gare su koma bakin aiki cikin gaggawa ko kuma a dakatar da aikinsu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe