31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Jerin jihohi 15 da basu biyan malamai ƙarancin albashi na N30,000

LabaraiJerin jihohi 15 da basu biyan malamai ƙarancin albashi na N30,000

Shekara uku bayan shugaba Buhari ya rattaɓa hannu akan sabon tsarin biyan albashi zuwa doka, malaman makaranta a makarantun firamare da sakandire a jihohi 15 har yanzu ba su san anayi ba, inda ba a fara biyan su mafi ƙarancin albashin na N30,000 ba.

Hakan na ƙunshe ne a wani bayani da ƙungiyar malamai ta ƙasa ta fitar. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Jerin jihohin da basu biyan ƙarancin albashin

Jihohin da basu biyan ƙarancin albashin na N30,000 sune:

1. Abia
2. Bayelsa
3. Delta
4. Enugu
5. Nasarawa
6. Adamawa
7. Gombe
8. Niger
9. Borno
10. Sokoto
11. Anambra
12. Imo
13. Benue
14. Taraba
15. Zamfara

Jihohin da ke biyan malamai mafi ƙarancin albashin N30,000

Haka kuma bayanin daga ƙungiyar malaman ya nuna cewa jihohi 15 ne kaɗai tare da birnin tarayya Abuja, ke biyan albashin mafi ƙaranci na N30,000 ga malaman firamare da sakandire.

Jihohin da ke biyan sabon tsarin na N30,000 sune:

1. Akwa Ibom
2. Ebonyi
3. Edo
4. Ekiti
5. Jigawa
6. Kano
7. Katsina
8. Kwara
9. Lagos
10. Ogun
11. Ondo
12. Osun
13. Oyo
14. Plateau
15. Rivers
16. FCT.

Jihohin Kogi da Cross River ba su biyan cikakken sabon ƙarin albashin, yayin Kaduna da Yobe suka koma amfani da tsohon tsarin biya na N18,000 na shekarar 2011.

Sabon tsarin na biyan N30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ya zama doka bayan da shugaba Buhari ya rattaɓa masa hannu a watan Afrilu, 2019, bayan an daɗe ana kai ruwa rana da ƙungiyar ƙwadago.

Malamin makaranta ya kwashe albashin sa wajen yin gyaran makarantar da yake koyarwa

A wani labarin kuma malamin makaranta yayi amfani da albashin sa wajen yin gyaran makarantar da yake koyarwa.

Shugaban makarantar firamaren Kwasi Nyarko Presbyterian Primary School, Richard Boakye Marfo, yayi amfani da kuɗaden da ake biyan sa wajen yin sabon fenti a makarantar domin ƙarawa makarantar kyau. Legit.ng ta rahoto

Makarantar wacce take a gundumar Upper West Akim District a cikin yankin gabashi, tana goga kafaɗa tsakanin ta da sauran makarantun yankin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe