31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Gazawar Buhari ta kashe kasuwar Bola Tinubu – Dino Melaye

LabaraiGazawar Buhari ta kashe kasuwar Bola Tinubu - Dino Melaye

Kakakin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, Dino Melaye, yace rashin taɓuka abin a zo a gani da shugaba Buhari yayi a karagar mulki ya kashe kasuwar ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na zama shugaban ƙasa.

Buhari ya shafawa Tinubu kashin kaji

Dino Melaye, wanda ya bayyana hakan a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV, yace gazawar da jam’iyyar APC tayi na samar da mafita kan halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki ya sanya gabaɗayan ƴan takarar ta sun zama baƙar haja mai wuyar sayarwa. Jaridar The Punch ta rahoto.

Yace:

Mun yi ayyuka da dama. Mun saurari ra’ayoyin mutane, mun tattauna da mutane, sannan wannan gwamnatin ta tallata Atiku ta hanyar gazawar ta.

A yau, ɗan takara mafi wahalar tallatawa shine ɗan jam’iyyar APC, ko da a matakin kansila, ɗan majalisar jiha, ɗan majalisar wakilai, ɗan majalisar dattawa ko gwamna.

Wannan shiyasa ba zaka iya kare Bola Ahmed Tinubu ba, ba zaka iya tallata Bola Ahmed Tinubu ba, ba zaka iya kamfen ɗin zaɓen Bola Ahmed Tinubu ba, ba tare da an maka kallon sakarai ba.

Dino Melaye ya bayyana abinda ya sa Atiku ya cancanta

Melaye ya kuma ƙara da cewa:

Atiku ya shirya kan sa domin zuwan irin wannan lokacin. Ko a cikin shekara 2 da suka wuce, shine kaɗai ɗan takarar da yaje ƙaro kwalin karatun sa, ya samo digirin digir (Master’s) daga wata jami’a a Cambridge. Don haka wane ɗan takara ne yafi shiryawa a fannin ƙwarewa, kyautatawa da kuma sanin mutane?

2023: Karon farko Atiku da Wike za su sulhunta

A wani labarin kuma ana shirin yin sulhu tsakanin Atiku da Wike.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, sun amince da kawo karshen sabanin dake tsakaninsu.

Sun cimma wannan matsaya ne a ranar Alhamis a wani taro da suka yi a Abuja a gidan tsohon ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Jerry Gana.
Wannan dai shi ne karon farko da shugabannin biyu za su gana tun bayan da Atiku ya yi watsi da Mista Wike ya nada gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe