34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Kotu ta yankewa basarake mai mata 12 hukuncin kisa

LabaraiKotu ta yankewa basarake mai mata 12 hukuncin kisa

An yanke wa wani basarake wanda shine dagacin ƙauyen Efen Ibom a ƙaramar hukumar Ika ta jijar Akwa Ibom, Cif Essien Matthew Odiong, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Basaraken, wanda ake kara kan laifuka huɗu na cin amana, an yanke masa hukuncin ne bisa kisan wani mai suna Udoma Udo Ubom. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

An samu basaraken da laifi dumu-dumu

A cewar hukuncin da mai shari’a Edem Akpan na babbar kotun jihar Akwa Ibom ya yanke, an samu basaraken da laifin kisan kai bayan da aka yiwa mamacin allura mai ɗauke da wani sinadari wacce tayi sanadiyyar mutuwar sa a ranar 26 ga watan Afrilu, 2017.

Abubuwan da suka jawo mutuwar Ubom dai shine ƴan’uwan sa sun zarge shi da maita, wanda daga nan dagacin ya sanya shi yin rantsuwa domin nuna gaskiyar sa.

Kotun ta ce:

Bayan ya fahimci aika-aikar da ya tafka, basaraken ya arce daga ƙauyen a shekarar 2017 sannan ya dawo a shekarar 2019, lokacin da ƴan sanda suka damƙe shi.

A cewar kotun wannan sinadarin da aka sanya a sirinji a jikin ɗuwawun mamacin shine silar mutuwar sa.

Bayanin yadda hukuncin zai kasance

Alƙalin ya yanke wa basaraken mai shekara 82 a duniya hukuncin kisa ta hanyar rataya, shekara bakwai a gidan kaso tare da aiki mai wahala bisa gudanar da haramtacciyar shari’a, sannan da shekara uku a gidan kaso bisa haɗa baki da wasu waɗanda har yanzu basu shiga hannun hukumomi ba.

Odiong yana da ƴaƴa 60 tare da matan aure 12.

Gwamna ya tuɓe rawanin basarake saboda halartar taron PDP

A wani labarin kuma gwamna ya tuɓe rawani basarake saboda halartar taron jam’iyyar adawa.

Gwamnan jihar Cross Rivers, Prof Ben Ayade, ya sauke basaraken Muri Munene na ƙasar Efut kuma sarkin Calabar South, Itam Hogan Itam, daga kan kujerar sa. Jaridar Punch ta rahoto.

Basaraken ya saɓa wa sashi na 30 sakin layi na 3 na dokar masarautun jihar Cross Rivers ta hanyar zuwa taron jam’iyyar PDP na yankin Cross River ta kudu, inda aka marawa wani ɗan takarar gwamna, Arthur Jarvis Archibong, baya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe