27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Ilimi:Jihar Legas ta ba da umarnin sake dawo da Darasin Tarihi cikin jaddawalin karatu a makarantu

LabaraiIlimi:Jihar Legas ta ba da umarnin sake dawo da Darasin Tarihi cikin jaddawalin karatu a makarantu
Lagos schools

Gwamnatin jihar Legas  ta ba da umarnin sake dawo da darasin Tarihi a matsayin “Darasi mai zaman kansa a cikin kananan aji na makarantun sakandare da kuma manyan aji.

An aika da takarda

A cewar wata takarda da aka aike wa masu makarantu masu zaman kansu tare da sanya hannun daraktan bincike a ofishin tabbatar da ingancin ilimi na ma’aikatar ilimi ta jihar Legas, Pelumi E.I, sabon ci gaban ya yi daidai da umarnin hukumar bincike da ci gaban ilimi ta Najeriya. Majalisar (NERDC).
Takardar ta kara da cewa, an sake bullo da wannan batu a cikin manhajar karatu ta kasa da kuma tsarin bai daya da ake yi a jihar Legas a makarantun firamare da kananan sakandare.

Gwamnati ta maida darasin wajibi ga makarantu

Gwamnati ta ce batun ya zama wajibi ga azuzuwan firamare da na kananan ajujuwan sakandare amma na manyan makarantun sakandare an maida shi zabi sonka.
Ga abinda takardar ta ce; “Ku sani cewa duk da cewa darasin (Tarihi) ya zama dole a azuzuwan firamare da na karamar ajin sakandare, amma zabi sonka ne a babbar ajin sakandire.
“Don haka, an kara ba ni umarni da in sanar da ku cewa ya kamata a koyar da darasin a matakin firamare na 1 da 2 da JSS 1 da 2 a zaman karatun 2022/2023.

Zakara :Valor Mbre dalibin da ya lashe jarabawar WAEC da JAMB a jihar Akwa Ibom

Valor Mbre Inyang dan asalin jihar Akwa Ibom ya burge mutane da dama a kafofin yanar gizo da kyakyawan sakamakon jarabawar sa. Valor wanda ya kasanceTsohon dalibin makarantar Top faith Schools, Akwa Ibom, ya cinye jarabawar sa ta WAEC inda ya lashe duka darussa 9 da ya zana . Bayan haka, ya sake lashe jarabawar joint Admission and Matriculation Board wato (JAMB)inda ya samu jimillar maki 343.

Kwamishinan yada labarai ya yaba wa yaron

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Akwa Ibom, Ini Ememobong, shine ya wallafa labarin a shafin sa na Facebook tare da hotunan sakamakon ya ce:
“Ina taya matashi dan asalin Akwa Ibom,Valor Inyang, murna wanda ya tabbatar wa duniya cewa daukaka ita ce kirarin mu. Ina addu’ar sauran Dalibai su da shi.” Valor shine dalibin da ya fi kowani dalibi samun sakamako inda ya kammala karatun sa a makarantun Topfaith, Valor shine dalibin da ya fi kowani dalibi samun sakamako inda ya kammala karatun sa a makarantun Topfaith, hotunan da aka yada a yanar gizo sun nuna lokacin da yake karbar lambar yabo yayin kammala karatun sa.

An tuntubi mahaifin yaron

Mahaifin Valour ya yi magana game da dansa
Lokacin da Legit.ng ta tuntubi mahaifin Valour, Mbre Inyang, ya bayyana jin dadinsa game da sakamakon dan nasa tare da godewa Ubangiji. Ya ci gaba da bayyana irin abubuwan da dansa ya yi a shekarunsa na firamare da sakandare wanda har ya kai ga samun tallafin karatu daga Gwamnatin Jihar Akwa Ibom. Mahaifin Valour ya kuma bayyana cewa dansa yana matukar burgesa saboda jajircewar sa wajen neman ilimi ingantacce.
Kalaman mahaifin Valor:
Na gode da kuka tuntube ni, na godewa Allah Ta’ala bisa abin da Ya yi wa iyalina. A gaskiya na yi matuƙar farin ciki da wannan lamari.” “Tun da ya fara makarantar firamare, ya ke daukan matsayin farko a ajinsa, shi ne ya fi kowani dalibai kokari a lokacin bikin yaye dalibai a makarantar firamare, inda ya lashe dukkan kyaututtuka.” “Ya wakilci jihar Akwa Ibom a gasar ilimin lissafi na makarantun firamare a Najeriya kuma ya samu guraben karo karatu, ya samu lambobin yabo na ilimi da dama, wani abu da ya fi daukar hankalin yarona shi ne ya mai da hankali sosai da jajircewa.”
Yan Najeriya sun yaba wa Valor Inyang

Mfonobong Asuquo ya ce: “Wannan matashin yana da hazaka kuma yana bukatar tallafin turawa kai tsaye zuwa manyan Makarantun Injiniya a Duniya kamar MIT, Stanford, UCLA ko Carnegie – Mellon ta Gwamnatin Jihar Akwa Ibom. Ta haka ne za a tayar da manyan gobe.”

Solomon Nse ya rubuta cewa: “Wannan shi ne abin da na taba yi wa WAEC da JAMB a waccan shekarar na yi maka murna. Alfahari da Akwa Ibom!”
Essy Akpan ya ce: “Magnificent! Barka da tauraron Akwa Ibom. Ka ci gaba da karya tarihi.”
Aniekan Brown ya ce: “Ina maka addua Ina taya ku murna ga tauraro mai tasowa.”

Michael Alfred ya ce: “Wannan yaron yana da ban mamaki sosai. Dukansu wassce da jamb suna da daraja. Babban farin ciki!”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe