34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Jerin murdaddun mata 5 da babu namijin da zai so dambe ya hada su

LabaraiLabaran DuniyaJerin murdaddun mata 5 da babu namijin da zai so dambe ya hada su

A wannan labarin za ku ji jerin mata guda 5 da su ka murde fiye da maza da dama kuma babu wani namijin da zai so dambe ya hada su don dukan tsiya za su yi masa, The Unkown Facts ta ruwaito.

  1. Colette Guimond
one
Colette Guimond

Fitacciya kuma kwararriyar mai motsa jiki ce a kasar Canada wacce ta kwashe shekaru tana sana’ar.

Tun tana da shekaru 26 ta fara motsa jiki, bayan shekaru 2 ta fara gasar dambe.

Guimond ta lashe gasar The Montreal a shekarar 1989 amma bata kai ga nasara a gasar kwararru ba. Bayan ta tafka hadari a 1997, sai ta dakatar da duk wata harkar motsa jiki.

A shekarar 2005 Guimond ta dawo dumu-dumu cikin harkar bayan lashe gasar daga abubuwa masu nauyi da kuma kasancewa mace mafi murdewa a Canada.

  1. Bregeta Bresavoc
two
Bregeta Bresavoc

‘Yar Slovenia ce kuma kwararra ce a harkar motsa jiki don tun tana da shekaru 14 a duniya ta fara daga nauyayan karafa.

Ta kula da saurayinta yana da wurin daga kayan nauyi ne a wurin horonsa na gida, daga nan ta yanke shawarar farawa.

Lokacin tana da shekaru 22 da haihuwa ta shiga gasar karfi da kuma daga nauyayan karafa inda ta zama ta hudu.

A shekarar 2004 ne ta shiga wata gasar motsa jiki inda aka dakatar da ita saboda ta na da fasalin maza. Duk da bata lashe gasar ba amma ta samu nasarar lashe wasu na daban kafin tayi murabus a shekarar 2013. Kuma har Ifbb ta nada mata mace mafi murdewa ta 5.

  1. Rene Campbell
three
Rene Campbell

Wannan mai motsa jikin ‘yar Birtaniya ce, kuma ta yi saurin murdewa kwarai. Ta fara shiga gasa ne bayan shekaru 4 da fara motsa jiki.

Matar mai yara 2 tana matukar son harkar motsa jiki har ta kai ga tana daga karfen da ya kai nauyin 280 pounds a ko wacce rana.

Don kara murdewa, tana cin abinci mai 4,200 calories a ko wacce rana, kuma tana hawa sikeli ne a duk lokacin da za ta ci abincin.

Campbell na da burin gwada gasa tare da maza, hakan yasa take matukar dagewa.

  1. Yolanda Hughes
four
Yolanda Hughes

Tun a makaranta take shiga gasar motsa jiki da wasanni kasancewar tana da burin zama ‘yar wasa idan ta kammala karatu.

Ta lashe gasa kala-kala wadanda ta ci nasara daban-daban tun a makaranta wanda har ta samu nasara aka dauki nauyinta na wani lokaci.

Bayan lokacin ya wuce ne ta ci gaba da motsa jiki inda ta zama kwararra a shekarar 1992. Daga nan ne ta yi aure ta koma kasar Jamus tare da mijinta, inda ta bude wurin motsa jiki.

A shekarar 1997 ne ta samu lambar yabo ta kasa da kasa, sannan a shekarar gaba ma ta kara samun lambar.

  1. Yaxena Oriquen-Garcia
five
Yaxena Oriquen-Garcia

‘Yar Venezuela ce kuma tana daya daga cikin masu motsa jiki mafi karfi da kuma ado. Ta fara motsa jiki ne a karshen shekarar 1980 da doriya har shekarar 1993 inda ta lashe gasar Central American Championship.

Hakan ya auku ne bayan kwashe shekaru da dama tana motsa jiki a ko wacce rana tare da shiga gasa iri-iri.

Ifbb ta nada Yaxena a matsayin mace mafi murdewa, kuma ko da ta kai shekaru 50 bata da niyyar dena daga karafa.

Har jibi tana matukar son harkar matsa jiki da duk wasu wasanni a wurin motsa jikinta da ke Florida.

Hotuna: Jerin azzaluman mata 8 da aka taba yi a tarihin duniya da irin muguntarsu

A wannan labarin za ku ji labarin jerin azzaluman mata da aka taba yi a tarihi, hotuna, sunaye, tarihi da nau’in muguntarsu kamar yadda shafin Unkown Facts na Facebook ya ruwaito.

  1. 1. Mary I ‘yar kasar Ingila

An fi saninta da Bloody Mary. Ta halaka rayukan masu zanga-zanga da dama yayin da take kokarin tabbatar da Katolika a Ingila a zamaninta.

Dokar da ta kakaba ce ta sanya aka babbaka masu zanga-zanga wurin 300 wadanda aka zarga da tayar da tarzoma.

Sai dai abin ban takaicin shine yadda ba doka bata yi aiki akanta ba duk da ta’addancin da ta jagoranta. Sai dai bayan ta mutu, an rushe tsarin katolikan da ta gina.

  1. 2. Aileen Wuornos

Ita ce ‘yar fashin babban titin da ake zargin ita ce mace ta farko a irin ta’addancinta a kasar Amurka. Ta harba sannan ta yi wa kusan maza 7 fashi da makami a Florida. Kuma ta yi zamani ne a 1980 da doriya zuwa farkon 1990 da doriya.

Kuma tana cewa ne duk wanda ta harba ta yi yunkurin kare kanta da kanta ne. Sai dai daga baya aka kama ta dumu-dumu da laifin halaka maza 6 sannan aka gurfanar da ita gaban kotu.

A shekarar 2002 ne aka yanke mata hukuncin kisa ta hanyar yi mata allurar guba. Bayan shekara daya ne aka bayyana tarihinta a wani fim wanda yayi fice mai suna “Monster” wanda ya bayyana muguntar ta.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe