34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Abinda yasa aka bani babban darektan yaƙin neman zaɓen Tinubu -Gwamna Lalong

LabaraiAbinda yasa aka bani babban darektan yaƙin neman zaɓen Tinubu -Gwamna Lalong

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya bayyana yadda akayi ya zama babban darektan yaƙin neman shugaban na ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Lalong yace saɓani da surutun da ake yaɗawa a wasu sassan ƙasar nan, naɗin shi ba domin a saka wa al’ummar Kiristocin Arewa bane bisa rasa kujerar mataimakin shugaban ƙasa. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Gwamnonin APC ne suka zaɓi Lalong yaja ragamar yaƙin neman zaɓen Tinubu

Da yake jawabi ga ƴan jarida a Abuja wurin nuna nasarorin da ya samu akan kujerar sa da kuma yin watsi da maganar da ake yaɗawa cewa an zaɓe shi ne yaja ragamar yaƙin neman zaɓen APC, saboda taƙaddamar tikitin Musulmi da Musulmi da ta baibaye jam’iyyar, Lalong yace gwamnonin APC sune suka zaɓe shi saboda girman matsayin sa na shugaba.

Yace bayan ɗan takarar jam’iyyar APC ya zaɓi mataimakin sa, gwamnonin sun zauna domin tattauna abu na gaba da za su yi.

Dalilin zaɓar sa

Yace gwamnonin sun shaida wa Tinubu cewa sun yi namijin ƙoƙari wurin ganin shugaban ƙasa ya fito daga Kudu, sannan sun yi tsammanin a shawarce su wurin ɗaukar mataimaki da babban darektan yaƙin neman zaɓe.

Dukkan su sun yarda cewa in jagoranci yaƙin neman zaɓen saboda nine shugaban gwamnonin Arewa, sannan kuma domin ni na kai su wurin shugaban ƙasa don ganin cewa an kai kujerar shugaban ƙasa kudu. Don haka ake kallona a matsayin jagora. Ba batun la’akari da addini bane. A cewae sa

Ganduje ya bayyana muhimmin dalilin da yasa Tinubu ya ɗauki musulmi a matsayin mataimaki

A wani labarin kuma gwamnan Kano, Ganduje ya bayyana dalilin da yasa Tinubu ya ɗauki musulmi a matsayin mataimaki.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yace ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zaɓi musulmi ne a matsayin abokin takarar sa domin kawar da muhimmanci na musamman da ake ba addini a siyasar Najeriya

Ganduje wanda yana a gaba-gaba cikin masu yaƙin neman zaɓen Tinubu, ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake magana da ƴan jarida a masallacin Juma’a na Unguwar Sabo, a Osogbo, babban birnin jihar Osun

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe