27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Bidiyo: Yadda aka cafke wata mata ta sace da haɗiye sarƙar N1.5m

LabaraiBidiyo: Yadda aka cafke wata mata ta sace da haɗiye sarƙar N1.5m

Wata mata mai halin ɓera ta sace sannan ta haɗiye sarƙar zinare mai tsadar gaske, wacce darajarta ta kai kimanin kuɗi Naira miliyan ɗaya da rabi (N1.5m) a wani shagon sayar da kayan alatu na kwalliya.

Dalilin da yasa ta haɗiye sarƙar

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa matar ta haɗiye sarƙar ne domin samun sauƙi wurin ficewa daga cikin shagon ba tare da asirin ta ya tonu ba har ya kai ga an kama ta.

Sai dai bata samu nasara ba inda shirin da tayi ya wargatse aka samu nasarar cafko ta sannan aka cigaba da bin diddigin abinda ta aikata.

Matar ta roƙi da kada a yi yamaɗiɗi da ita a yanar gizo

A lokacin da ake tuhumar ta, an ji tana roƙon wanda yake ɗaukar bidiyon ya taimaka ya rufa mata asiri kada ya sanya bidiyon a shafin Facebook.

Cikin magiya da nuna yanayi na tausayi matar ta nemi da a taimake ta kada a sanya ta a idon duniya asirin ta ya tonu, inda ta nemi ko albarkacin yaran ta samu ta ci kada a watsa ta a duniya.

Ka taimaka min yallaɓai, kai ma kana da yara. Ka taimaka kada ka sanya ni a Facebook. Ta roƙa cikin harshen Yarbanci

Ƴan sanda sun cafke riƙaƙƙen ɓarawo mai yaudarar mata zuwa otal yana musu sata

A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun cafke wani gawurtaccen ɓarawo mai yaudarar ƴanmata zuwa otal yana tafka musu sata. Ɓarawon ya aikata wannan mummunar sana’ar ga mata da yawa.

Jami’an ƴan sanda na Surulure a jihar Legas sun cafke wani ɓarawo mai suna  Ifeanyi Odieze Ezenagu mai shakaru 34 bisa zargin tafka laifin sata ga mata daban-daban, inda yake kwace musu ɗan abin hannun su. 

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa a wata sanarwa da kakakin hukumar ƴan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya fitar, yace wanda ake zargin ya sacewa matan wayoyin hannu ƙirar iPhone 12 guda uku, iPhone 11 Pro Max guda biyu, iPhone XR guda ɗaya, wayar Nokia guda ɗaya, agogon hannu guda ɗaya sannan da sarƙar zinare guda ɗaya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe