An kai hari ga fitaccen marubucin nan mao suna Salman Rushdie, wanda aka kwashw tsawon lokaci ana yi masa barazanar kisa bisa wani littafin sa da ya rubuta mai suna The Satanic Verses.
Jaridar BBC Hausa ta rahoto cewa an dai kai wa marubucin harin ne a yayin da yake jawabi a wani wurin taro a Jihar New York da ke Amurka.
Marubucin mai shekara 75 a duniya, wanda ya taɓa lashe kyautar The Booker Prize, yana yin jawabi ne a cibiyar Chautauqua yayin da aka kai masa wannan hari.
Yadda aka kaiwa marubucin hari
Shaidun ganau ba jiyau ba sun ce sun ga wani mutum ya ruga a guje ya hau kan dandamalin da marubucin yake jawabi inda ya riƙa naushi yana kuma daɓa wa Mr Rushdie wuƙa a yayin da ake gabatar da shi gaban jama’a.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan yanar gizo ya nuna mahalarta taron sun ruga a guje kan dandamalin domin kai masa ɗaukin gaggawa.
Sai dai bayanan da aka samu sun nuna cewa akwai alamun an daɓa masa wuka a wuya.
Alamu sun nuna cewa an ji wa Rushdie rauni da wuƙa a wuyansa. A cewar sanarwar jami’an ƴan sanda
An garzaya da shi wani asibiti a cikin jirgi mai saukar angulu, ko da yake ba a samu cikakken bayani game da irin girman raunin da aka ji masa ba.
Marubucin ɗan asalin ƙasar Indiya ya shahara ne bayan ya rubuta wani littafi mai suna Midnight’s Children a shekarar 1981, wanda ya samu karɓuwa sosai inda aka sayar da kwafe fiye da miliyan a ƙasar Birtaniya kaɗai.
Ya shiga ɓuya bayan wallafar wani littafin sa
Sai dai Mr Rushdie ya shiga ɓuya har ta tsawon shekara 9 bayan wallafar littafin sa na huɗu, The Satanic Verses wanda ya rubuta a shekarar 1981.
Littafin ya gamu da fushin al’ummar musulmai, waɗanda ke kallon sa a matsayin ɓatanci ga addini, inda aka haramta sayar d littafin a wasu ƙasashe.
Shekara ɗaya bayan wallafa littafin, Shugaban addinin ƙasar Iran Ayatollah Khomeini ya sanya ladan $3m (£2.5m) ga duk wanda ya kashe Mr Rushdie.
Mutane da dama ne suka mutu sakamakon tarzomar da ta barke a dalilin wallafa littafin, ciki har da wasu da suka fassara littafin zuwa wasu harsunan.
Ɓatanci: Matasa sun bazama neman wata mata bisa zagin Annabi (SAW) a Bauchi
A wani labarin na daban kuma matasa sun bazama neman wata mata bisa zargin yin ɓatanci ga Annabi (SAW) a jihar Bauchi.
An rauna ta wani fasto sannan an ƙona gidaje a yankin Katangan ta ƙaramar hukumar Warji a jihar Bauchi, bisa zargin yin ɓatanci ga annabi Muhammad (SAW).
Jaridar Punch ta rahoto cewa rikicin ya fara ne lokacin aka yaɗa wani sako a yanar gizo cewa wata mata kirista a garin ta yi ɓatanci ga addinin musulunci.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com