27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

‘Yar TikTok ta sha caccaka bayan wallafa bidiyonta tana rusa kuka bayan tafka hadari

Labarai'Yar TikTok ta sha caccaka bayan wallafa bidiyonta tana rusa kuka bayan tafka hadari

Jama’a sun yi caa akan wata budurwa wacce babu dadewa da tafka mummunan hadari a ranar 10 ga watan Augusta, ta dauki kanta bidiyo inda ta wallafa a TikTok, LIB ta ruwaito.

Mutane da dama sun tausaya mata yayin da wasu su ka dinga caccakarta su na ganin cewa bata cancanci tausayawa ba tunda har ta iya tura bidiyon da ta dauka da kanta a TikTok.

A hadarin da ta yi an ga yadda jini ya dinga kwarara daga kanta kasancewar ta ji mummunan rauni.

Da farko mutane sun yi kokarin taimaka mata da sauran wadanda su ka yi hadarin, kuma an ganta tana kuka yayin daukar bidiyon.

A bidiyon an ga abin hawa a gefe wadanda su ka yi hadarin.

Har ila yau ta kara wallafa bidiyonta kwance a gadon asibitin yayin da kanta, hannu da guiwarta ke nade da bandeji.

Mutane da dama sun tausaya mata su na taya ta murna da bata rasa ranta ba, wasu kuma sun zargeta da yin bidiyon don daukar hankalin jama’a.

Sun bukaci danin dalilinta na daukar bidiyon maimakon ta dakata har sai ta samu lafiya.

Mahaifin wata ‘yar TikTok ya kwanta dama bayan ganin bidiyonta tana rawar wakar batsa

Wata ‘yar TikTok ta yi sanadiyyar ajalin mahaifinta bayan ya ga bidiyonta tana rawa da wakokin batsa da zage-zage a kafar.

Ganin bidiyon nata ke da wuya, wanda dama shi malami ne na addini, ciwonsa ya tashi yace ga garinku.

Kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito bidiyon wani mutum yana bayani, ya ce wani malamin addini ne ya ga diyarsa tana rawar TikTok wanda hakan ya yi ajalinsa.

Kamar yadda mutumin ya bayyana, daya daga cikin daliban malamin ya dade yana ganin diyarsa tana rawar amma sai yana kokwanton idan diyar malamin ce.

Ya ci gaba da shaida cewa watarana ya ga yarinyar ta saki wani bidiyo na rashin kyautawa, sai ya dauka ya nunawa mahaifinta bayan sun gama karatu.

Ya bayyana cewa an nuna masa bidiyoyi fiye da hamsin na diyarsa wadanda take nuna tsiraicinta da kuma rashin tarbiyya.

Ya bayyana cewa bayan ya tsare diyar da matarsa akan yadda su ka ci amanarsa yayin da su ka yi cirko-cirko, ya yanke jiki ya fadi kasancewar yana da hawan jini.

Ya ce bayan ya yi kwanaki a asibiti ya mutu sanadiyyar wannan takaici da bakin cikin da diyarsa ta sanya sa a ciki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe