34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Gobara ta barke a Majalisar Dokoki ta kasa ta kona takardu da wasu kayan ofis

LabaraiGobara ta barke a Majalisar Dokoki ta kasa ta kona takardu da wasu kayan ofis
WhatsApp Image 2019 07 24 at 23.09.09
National Assembly

Takardu da kayan ofis da dama sun lalace biyo bayan wata gobara da ta tashi a sabon reshen majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Majalisar, Emmanuel Agada, ya fitar a ranar Alhamis, gobarar ta tashi ne a daki mai lamba 227 a sabon reshe na Majalisar Wakilai da misalin karfe 6 na yamma .
Mista Agada ya ce ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki amma hadin gwiwar ma’aikata da jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya sun taimaka wajen takaita yaduwar gobarar.
Sanarwar ta ce “An kashe gobarar tare da taimakon ma’aikatan da ke bakin aiki, inda nan take suka kutsa cikin ofishin da abin ya shafa tare da tura na’urorin kashe gobara a kasa kafin isowar jami’in kashe gobara.”
Ya bayyana cewa ana ci gaba da tantancewa wanda zai iya shafar ‘yan majalisa da ma’aikatan da ke amfani da wannan reshe na wani lokaci.
“Ana sa ran, bayan tantancewar da hukumar kashe gobara ta yi da hukumar kula da gidaje da kuma daraktocin ayyuka, za a dawo bakin aiki ga dukkan manyan jami’an majalisar wakilai da ofisoshin mambobi, nan take,” sanarwar ta bayyana.
A halin yanzu Majalisar Dokoki ta Kasa tana wani gagarumin gyare-gyare, musamman fadar White House, wadda ke da Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da wasu ofisoshi.

Ɓarayi sun shiga gidan gwamnatin jihar Katsina, sun sace maƙudan ƙuɗaɗe

Ana zargin wasu ‘Ɓarayi’ sun kutsa gidan gwamnatin jihar Katsina sun sace kudi har naira miliyan N31m.

Wannan shi ne karo na biyu da aka yi irin wannan ta’asar ta sata a gidan gwamnati, wanda shine yakamata ya kasance ginin da yafi kowanne tsaro a faɗin jihar.

An taɓa tafka sata a ofishin sakataren jihar Katsina
A shekarar 2020, an sace maƙudan kuɗaɗe da suka kai miliyan N16m a ofishin Sakataren gwamnatin Katsina (SSG).

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa wata majiya daga gidan gwamnatin ta shaida cewa lamarin satar kuɗin ya faru ne tun a ranar 31 ga watan Yuli, 2022.
Majiyar wacce ta nemi a sakaya sunan ta tace wasu mutane da ba’a san ko suwaye ba sun kutsa ofishin mai kula da kuɗi na gidan gwamnatin, suka yi awon gaba da wasu kuɗi a cikin buhu.

A cewarsa, satar ta auku ne da daddare lokacin mai kula da kuɗin, Salisu Batsari, yana cikin ofishin.

Banga kyamarar CCTV ba amma kunsan tana daya daga cikin abubuwan da yan sanda zasu buƙata. Naji ance kyamarar ta ɗauki wani mutum ya rufe fuskarsa lokacin da ya kutsa Ofis ɗin ta cikin taga.” A cewar sa

An tabbatar da aukuwar lamarin
Wani hadimin gwamnan jihar Katsina, Al’Amin Isa, ya tabbatar da sace kudin ga manema labarai amma bai ce komai ba game da adadin kuɗin da aka rasa ba.
An miƙa rahoton lamarin ga ƴan sanda sannan ana cigaba da gudanar da bincike

Isa ya ƙara da cewa gwamnatin da hukumar ƴan sanda na kan bincike game da satar kuma babu tantama duk wanda ya aikata zai fuskanci fushin hukuma.

Yace a lokacin da lamarin ya auku da farko, gwamnati ta ɗauki matakai domin daƙile sake aukuwar hakan amma mutanen na da shegen wayau.

Ƴan sanda ba su ce komai ba kan lamarin
Duk da kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Gambo Isa, bai dawo da saƙon da aka tura a wayar sa domin jin ƙarin bayani dangane da lamarin, majiyar gidan gwamnatin ya ce an kama wasu jami’ai amma an sake su.

A ranar Litinin da gwamnati ta fahimci an sace kuɗin, cikin gaggawa ta shigo da ƴan sanda suka fara bincike. Mai kula da kuɗi da wasu ma’aikata da masu gadi dake aiki a ranar ƴan sanda sun gayyace su domin amsa tambayoyi.”

Da aka tambaye shi ko da gaske ƴan sanda sun saki waɗanda ake zargin, sai ya kada baki yace ba shi da masaniya kasancewar ba ya daga cikin masu yin binciken.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe