
‘Yar wasan Ghana kuma mai wayar da kan jama’a Rosemond Brown, wacce aka fi sani da Akuapem Poloo, ta fito ta bayyan dalilin ta na sauya sheka daga addinin Kirista zuwa Musulunci. Jarumar kwanan nan ta sanar da sauya shekar ta zuwa addinin musulunci, kuma hakan ya jawo cece-kuce tsakanin jama’a. Poloo ta raba bidiyo a shafinta na Instagram tana bayyana dalilin da yasa ta sauya.
Ta ji dadin sauya shekanta
Ta bayyana jin dadin ta na zama musulma sannan ta roki ‘yan Ghana da su mutunta ra’ayin ta Jarumar dai ta dau damarar killace jikin ta,tare da daukar alkawarin daina bayyana tsiraicin ta.
Zata cigaba da rike dandalin ta
Sai dai zata ci gaba da rike sunan dandalin ta na yanar gizo tunda tace tayi magana da mallamin ta kan cewar sunan dandalinta bai saba wa duk wata ka’ida ta Musulunci ba, saboda haka zata cigaba da amfani da shi.
Martanin masu amfani da shafukan zumunta
A karon farko da akayi comment akan post din ta….Kada ki bari kowa ya baki shawara yadda zaki sa kaya..Abin da nake rokonki shine sallolinki guda 5 ki rike.Allah yana kallon zuciyar ki
rashkele2000 ya rubuta: Kai gaskia kinyi kyau cikin mayafi Allah ya kara albarka ya miki jagora
Miztoby yayi sharhi: kowane addini kika koma ina tare da ke ,dole mutum ya soki da duk abin da kuke yi ko zaba❤️❤️
An aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mata 3 a Iran bisa halaka mazajen su
Wata amarya mai ƙananan shekaru ƴar ƙasar Iran wacce ta halaka mijin da aka tilasta mata aure tana da shekara 15 a duniya, na daga cikin mata uku waɗanda aka aiwatarwa da hukuncin kisa bisa halaka mazajen su a cikin wannan satin.
Soheila Abadi, mai shekara 25 yanzu, an rataye ta a gidan kurkuru bayan an yanke mata hukunci bisa halaka mijinta akan ‘saɓanin iyali’ a cewar bayanan kotu. Shafin LIB ya rahoto.
An kuma aiwatarwa da wasu mata biyun hukuncin kisa a ranar Laraba bisa laifin halaka mazajen su.
Kotuna ba suyi wa matan da suka halaka mazajen su adalci a ƙasar
Masu rajin kare haƙƙin bil’adama sun yi iƙirarin cewa kusan duk lokacin da mata suka halaka mazajen su, to ana cin zarafin su ne a gida amma kotunan ƙasar Iran basa la’akari da hakan.
Matan guda uku na daga cikin mutane 32 da aka rataye a ƙasar a cikin satin da ya gabata.
Ana yawan aiwatar da hukuncin kisa a Iran
Hakan na zuwa a yayin da ake daɗa samun ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar, inda aƙalla mutum 251 aka kashe a farkon watanni 6 na wannan shekarar. A cewar rahoton Amnesty International.
Ana yawan aiwatar da hukuncin kisa a Iran
Hakan na zuwa a yayin da ake daɗa samun ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar, inda aƙalla mutum 251 aka kashe a farkon watanni 6 na wannan shekarar. A cewar rahoton Amnesty International.
Yawan mutanen ya ninka adadin da aka kashe a shekarar da ta gabata a irin wannan lokacin
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com