24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Yadda matashi ya halaka matarsa saboda ta shanye masa Koko

LabaraiYadda matashi ya halaka matarsa saboda ta shanye masa Koko
  • Wani matashi a Jihar Neja ya halaka matarsa har lahira saboda rikicin da ya balle tsakaninsu saboda koko
  • Lamarin ya faru ne a Kauyen Kadaura da ke karkashin karamar hukumar Rafi da ke jihar
  • An samu bayanai akan yadda ya fara da lakada mata bakin duka wanda yayi sanadiyyar mutuwarta

Wani matashi mai shekaru 20 ya halaka matarsa bisa rikicin da su ka samu saboda Koko kamar yadda majiyoyi su ka tabbatar, Amihad.com ta ruwaito.

An samu labarin yadda lamarin ya faru a kauyen Kadaura da ke Karamar hukumar Rafi, inda matar ta rasa ranta bayan mijinta ya zane ta.

Bayan cin bakin dukan ne ta kwanta rai a hannun Allah wanda daga bisani ta rasa ranta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa:

“Wanda ake zargi ya riga ya amsa laifinsa inda yace karamin sabani su ka samu tsakaninsa da matarsa saboda koko wanda hakan yasa ya dake ta.

“Take anan ta fadi rashe-rashe wanda aka zarce da ita asibitin Wushishi rai a hannun Allah daga nan likitoci su ka tabbatar ta rasu.”

Kakakin rundunar ‘yan sanda ya bayyanawa manema labarai cewa yanzu haka matashin yana hannun ‘yan sanda a babban ofishinsu da ke Kagara yana amsa tambayoyi.

A cewar Abiodun, bincike ya kammala kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

An aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mata 3 a Iran bisa halaka mazajen su

Wata amarya mai ƙananan shekaru ƴar ƙasar Iran wacce ta halaka mijin da aka tilasta mata aure tana da shekara 15 a duniya, na daga cikin mata uku waɗanda aka aiwatarwa da hukuncin kisa bisa halaka mazajen su a cikin wannan satin.

Soheila Abadi, mai shekara 25 yanzu, an rataye ta a gidan kurkuru bayan an yanke mata hukunci bisa halaka mijinta akan ‘saɓanin iyali’ a cewar bayanan kotu. Shafin LIB ya rahoto.

An kuma aiwatarwa da wasu mata biyun  hukuncin kisa a ranar Laraba bisa laifin halaka mazajen su.

Kotuna ba suyi wa matan da suka halaka mazajen su adalci a ƙasar

Masu rajin kare haƙƙin bil’adama sun yi iƙirarin cewa kusan duk lokacin da mata suka halaka mazajen su, to ana cin zarafin su ne a gida amma kotunan ƙasar Iran basa la’akari da hakan.

Matan guda uku na daga cikin mutane 32 da aka rataye a ƙasar a cikin satin da ya gabata.

Ana yawan aiwatar da hukuncin kisa a Iran

Hakan na zuwa a yayin da ake daɗa samun ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar, inda aƙalla mutum 251 aka kashe a farkon watanni 6 na wannan shekarar. A cewar rahoton Amnesty International.

Yawan mutanen ya ninka adadin da aka kashe a shekarar da ta gabata a irin wannan lokacin.

Daga cikin mutum 251 da aka halaka, 146 daga ciki masu laifin kisan kai ne, sannan aƙalla 86 masu laifuffukan ƙwayoyi ne wanda bai cancanci hukuncin kisa ba a dokar ƙasa da ƙasa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe